Shugaban gwamnatin rikon kwarya a Burkina Faso Michel Kafando ya ce ya koma kan mulki bayan juyin mulkin da sojin da ke kula da fadar shugaban kasar suka yi masa.
Kafando ya bayyana haka ne a daidai lokacin da mutumin da ya jagoranci juyin mulkin, Janar Gilbert Diendere ke kan hanyar sa ta tarbar shugabannin kasashen kunigyar ECOWAS da suka je kasar domin shaida masa ya sauka daga mulki.
A ranar Talata, sojin da ke tsaron fadar shugaban kasar sun sanya hannu a kan yarjejeniya da sojin kasar domin a kauce wa rikici.
Sojin da ke tsaron fadar shugaban kasar sun yi alkawarin koma wa bariki, yayin da su kuma sauran sojin kasar suka yi alkawarin janye wa daga babban birnin kasar,
Sojin da ke tsaron fadar shugaban kasar suna biyayya ga Blaise Compaore, shugabab da aka tumbuke daga kan mulki bayan wata zanga-zangar kin-jinin gwamnatinsa.
Title :
Michel Kafando Ya Koma Kan Mulki A Burkina Faso
Description : Shugaban gwamnatin rikon kwarya a Burkina Faso Michel Kafando ya ce ya koma kan mulki bayan juyin mulkin da sojin da ke kula da fadar shugab...
Rating :
5