TAMBAYA TA 1702
********************
AssalaMu alaykum malam Allah yasaka maka da aljannah akan alkhayrin da kake yadawa awannan dandali mai albarka.malm inaso ataymakamin da addu'a da kuma magani akan wan an cuta datake damuna malam nakasance da nakan yi wata UK hudu banyi al'adanaba kuma idan yatashi zuwa yana jimawa sai idan naje asibiti sannan subani magani ko allura kafin yatsaya har nayi aure a haka bai bariba har saida akayimin wakin ciki sannan nasamu NA haihu to yanzu kuma duk lokacin da Nazo yin al'ada INA fitar da wani abu gurbatacce kafin daga baya jinin yafara zuwa mai yauki.kumq kawanaki al'adan kwana takwas ne to wannan karon yakai sati ina fitarda gurbataccen sannan jinin yazo kuma yahaura kwana shabiyar nasha maganin asibiti,yayi kamar yatsaya amma idan natsuguna ina ganin sa daga baya kuma yafara zuba.
To malam ya zanyi da Ibadana.idan har lokacin danakeyi yasake zagayowa jin in baitsayaba,sannan idan zan samu ataymakamin damagani Wanda zanrabu da wannan matsalar.nagode
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Wannan matsalar rikicin jinin al'adar, mata da yawa suna fama dashi. kuma akwai dalilai masu yawa da suke kawoshi. (kamar yadda nayi bayani acikin amsar wasu tambayoyi irin wannan).
Abinda zakiyi shine ki samu ararrabi ki hada da Qustul Hindi da Garin Hulba. ki gaurayasu daidai da daidai.
Ki rika diban cokali guda kina dafawa da ruwa kofi guda. kina sha da safe kafin ki karya. Da dare ma kafin kici abinci sai ki sake dafawa kisha.
Zaki sha har tsawon sati biyu ko uku. In sha Allahu jinin zai daidaita. Kuma zai dena zuwa da mummunan kamanni.
Duk matar da jininta yazo har ya haura kwana sha biyar (15) bai dauke ba, zatayi wanka ne taci gaba da yin ibadarta. Wannan jinin ya zama na jinya kenan. Kuma zuwansa Ba zai hanaki Mu'amala da maigudanki ba.
Sai dai idan lokacin da kika saba yin haila ya zagayo, to zaki dena yin sallah ko azumi har sai kwanakin sun wuce sannan kici gaba.
Kuma zaki rika hada azahar sa La'asar kiyi wabka kafin kiyisu. hakanan Magriba da Isha'i. Hakanan ita mq asubah.
WALLAHU A'ALAM.