Mata 12 na yan Boko Haram sun mika kansu ga yan kungiyar Civilian JTF a karamar hukumar Askira-Uba dake Jihar Borno.
A cewar wani dan kungiyar civilian JTF, Apagu Istifanus, daga tsakanin 31 ga watan Agusta zuwa 1 ga watan Satumba, Mata 4 ne suka mika kansu saboda Mazajen su ba su iya ciyar dasu. 2 daga cikin su ma nada ciki.
Istifanus yace: “A ranar Litinin, guda 4 ne suka zo daga cikin su. Bayan da muka yi masu bincike, sai suka ce mazajen su ne basu iya ciyar dasu. Sannan akwai mata da yawa cikin daji suma suna nana tafe. Su dai mun kaisu Biu domin karin bincike.
“A jiya kuma, 8 ne suka taho wasu da cikin watanni ma. Sunce ya’yan su na Ngude a karamar hukumar Damboa. Su dai mun mika su zuwa Mubi.”
Dan kungiyar sa kan yace an kama matan ne saboda nasarar da sojoji suka samu a wannan yan kwanakin wajen dakila kaima yan kungiyar abinci.
Wani Soja wanda baya so a bayyana sunan shi ya fadi cewa: “Mu bamu zuwa muna gaya ma yan jarida abunda muke ciki. Amma lallai mun kusa kawo karshen yan Boko Haram.”
Title :
Matan 12 Na Yan Boko Haram Sun Mika Kansu
Description : Mata 12 na yan Boko Haram sun mika kansu ga yan kungiyar Civilian JTF a karamar hukumar Askira-Uba dake Jihar Borno. A cewar wani dan kungi...
Rating :
5