Manchester United ta samu nasara a kan Sunderland da
ci 3-0 a gasar Premier wasan mako na bakwai da suka
kara a Old Trafford ranar Asabar.
United din ta fara cin kwallon ta hannun Depay, sannan
Wayne Rooney ya ci ta biyu, bayan da ya yi wasanni 11
bai zura kwallo a raga ba.
Daf da za'a tashi daga karawar ne Juan Mata ya ci wa
United kwallo ta uku da hakan ya ba ta damar hada maki
uku a fafatawar.
Da wannan sakamakon United ta dare mataki na daya a
kan teburin Premier da maki 16, bayan buga wasanni
bakwai.
Sunderland kuwa tana matsayi na karshe na 20 a teburin
da maki biyu kacal, za kuma ta buga wasan gaba da
West Ham.