Shugaban kungiyar Real Madrid ya ce Manchester United ba ta da "gogewa" a kasuwar musayar 'yan kwallo, shi ya sa David De Gea bai koma Real Madrid ba.
Florentino Perez ya ce lamarin ya yi daidai abin da ya faru a Fabio Coentrao da kuma Ander Herrera a shekara ta 2013.
Perez ya ce "Basu goge ba."
"Haka abin ya kasance da Coentrao da kuma Herrera."
Real Madrid da Manchester United sun zargi juna a kan batun kasa kulla cinikin De Gea.
Kungiyar ta Spain ta ce ta yi iyaka kokarinta domin sayen golan mai shekaru 24 amma sai aka samu kuskure cikin minti biyu.
Title :
Manchester United ba ta 'goge' ba - Perez
Description : Shugaban kungiyar Real Madrid ya ce Manchester United ba ta da "gogewa" a kasuwar musayar 'yan kwallo, shi ya sa David De Gea ...
Rating :
5