Manchester United ta sayi dan kwallon Monaco, Anthony Martial kan kudi £36m.
Monaco ta bai wa Martial mai shekaru 19, wanda Arsenal ta dade tana zawarci izini a ranar Litinin da ya je Old Trafford domin a duba koshin lafiyarsa.
Dan wasan ya ci kwallaye takwas daga wasanni 31 da ya yi a gasar Faransa wato Ligue 1 a bara.
Martial ya zama dan wasa na uku da United ta dauka mafi tsada a tarihi, bayan Angel Di Maria da ta biya £59.7m daga Real Madrid da kuma Juan Mata da ta dauko daga Chelsea kan kudi £37.1m.
Dan wasan ya fara murza leda a Lyon a matsayin kwararren dan wasa a watan Disambar 2012, daga nan ya koma Monaco da taka leda a watan Yunin 2013.
Title :
Man United ta sayi Martial kan kudi £36m
Description : Manchester United ta sayi dan kwallon Monaco, Anthony Martial kan kudi £36m. Monaco ta bai wa Martial mai shekaru 19, wanda Arsenal ta dade...
Rating :
5