Malam Yusha'u Ibrahim
Malam Yusha’u Ibrahim kofar Waika, malami ne da ke koyar da masu ido a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi a Kano, duk da cewa yana da damuwar rashin gani amma hakan bai hana shi neman ilimi ba, inda har ya kai ga samun digiri na biyu, don haka yake ganin babu wani abu da zai gagari mai bukata ta musmaman matukar mutum yana numfashi. A tattaunawarsa da Aminiya ya yi kira da a samar da dokar da za ta ware wani kaso ga masu bukata ta musamamn a dukkanin ma’aikatun gwamnati da sauran abubuwa. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so jin takaitaccen tarihin rayuwarka?
Yusha’u: An haife ni a unguwar Chediyar ‘yan, gurasa cikin Birnin Kano. Na fara yin karatuna na firamare a makarantar Firamare ta Malam Aminu Kano da ke Sudawa. Wata rana da aka yi hutu a shekarar 1979 sai na yi rashin lafiya inda na yi kyanda bayan na warke sai na rasa gani. Hakan ya sa bayan mun koma hutu sai wasu malamaina suka shawarci mahaifina da ya kai ni makarantar masu bukata ta musamman da ke Tudun Maliki. Jin cewa makarantar ta kwana ce sai mahaifina ya ki amincewa, sai dai bai bayyana musu dalilinsa na hakika ba, inda ya ce musu mahaifiyata ce ba ta amince ba.
Ana cikin haka sai Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa. To daga baya sai mahaifiyata ta sa aka sanya ni makarantar Tudun Maliki inda na fara daga firamre aji daya. Bayan na gama firamare da karamar sakandire sai na shiga makarantar babbar sakandare ta Wudil. Muna wannan makaranta sai gwamnatin Jihar ta rushe makarantar. Daga nan aka mayar da ni Makarantar Horon Malamai ta Kano. Ina wannan makaranta saboda yanayin da nake ciki sai ya zama ina makara wajen zuwa makarantar, don haka na nemi canji aka mayar da ni makarantar Horon malamai ta Minjibir wacce ta kasance ta kwana ce. Anan na kammala sakandare dina a shekarar 1993.
Bayan na kammala sai na fara neman aiki, a shekarar sai na nemi aiki na fara koyarwa a karkashin ma’aikatar ilimi ta karamar Hukumar Dala. Daga baya sai na ga ya kamata na koma makaranta sai na sayi fom din Kwalejin Ilimi ta gwamnatin Tarayya da ke Kano. Amma sai suka ce su ba su taba koyar da dalibai marasa gani ba, to da yake mu biyu ne muka nema sai suka dauki wancan bisa sharadin za su gwada idan ya yi kokari to ni ma za su dauke ni. Allah cikin ikonsa wanan dalibin ya gama cikin nasara, don haka suka dauke ni, inda na kammala karatuna a 2003.
Bayan na koma na ci gaba da aiki, a shekarar 2005 sai na koma makaranta, inda na yi digiri a bangaren Special Education, inda na kammala a shekarar 2008. A shekarar 2009 sai na ga akwai bukatar in karo karatu, inda na yi digiri na biyu a bangaren Special Education.
Ina nan ina koyarwa a makarantar firamare sai na ji ina son in ci gaba da aikin koyarwa amma a manyan makarantu, don haka sai na nemi aiki a Kwalejin ilimi ta Tarayya (FCE) Kano, sai dai ban samu ba. Lokacin da gwamnatin Jihar Kano ta tashi daukar malami a manyan makarantun jihar sai na nama, nan ma dai ban samu ba. Da za a sake dauka sai na ce ba zan nema ba, amma sai wani abokina da muka yi karatu da shi ya karfafe ni da in nema, don haka na sake nema, inda kuma Allah Ya sa na dace aka dauke ni a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi a shekarar 2014.
Aminiya: Kasancewar duk da damuwar rashin ganida kake da ita, amma ga shi har ka yi digiri na biyu kana kuma koyarwa a daya daga cikin makarantun Jihar Knao, mene ne sirrin hakan?
Yusha’u: Ba wani siriri ba ne da ya wuce yarda da kai. Har kullum ina ganin cewa zan iya yin duk wani abu da mai ido zai yi, matukar ba nuna shi za a yi ba. A ganina nakasa ba a ta hana mutum kai wa ga cikar burinsa na rayuwa ba.
Muna da rubutu iri biyu. Na farko shi ne wanda muke zanawa da hannu, wanda ake kira brai,l sai wanda ya iya shi ne zai iya karantawa. A lokacin da nake karatu na fi yin amfani da brail wajen rubuta lacca, amma idan zan bai wa dalibai na kan buga da kwanfuta.
Babu shakka a lokacin da nake karatu na yi karo da matsaloli da dama, amma kuma hakan bai hana na ci gaba da neman ilimi ba har Allah Ya sa na samu cikar burina. Abin da ya sa ba na damuwa shi ne gani na yi masu idon ma haka suke fama da matsaloli ballantana marasa shi.
Tun farko ni mutum ne mai sha’awar aikin koyarwa, hakan ya sa duk karatun da na yi a bangaren koyarwa na yi shi, tun daga sakandire har digiri na biyu.
A ganina nakasa ba zai zama hujja ga mutum ya ki neman abin da yake so a rayuwa ba. Mutane na mamakin yadda nake koyarwa. Ina ganin in har zan iya koyarwa a matakin firamare wanda yake bukatar sai malami ya zaga aji don tabbatarwa. Ina ganin babu dangantaka tsakanin bara da nakasa.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwamnati wajen ganin ta inganta rayuwar musu bukata ta musamman?
Yusha’u: Ina kira ga gwamtani da ta samar da makarantu don masu bukata ta musamamn, kasancewar har yanzu makaranta guda daya ce rak a Kano, wato ta Tudun Malili. Idan kin duba wannan makaranta an yi ta ne a shekarar 1979 , amma tun daga wannan lokaci ba a sake yin wata ba.
Haka kuma akwai bukatar a samar da kayan aiki ga makarantun, domin har yanzu babu kwamfutoci na musamman a makarantar Tudun Malikin ma.
Bincike ya nuna cewa masu bukata ta musamman suna daukar kashi 40 na al’ummar jihar, amma idan ka duba babu wani abu da ake musu na a-zo-a-gani. A Najeriya damar da ke ga masu bukata ta musamman takaitattu ne, saboda ba a ba su ilimi ba ballantana a dauke su aiki. Idan ka bai wa mutum ilimi ka ba shi kashi 90 na rayuwarsa.
Su ma ‘yan majalisa ina kira gare su da su samar da wata doka da za ta kula da muradun masu bukata ta musamman. Misali, ya zama cewa dukkaknin ma’aikatu da hukumomin gwanmati an ware wasu guraben aiki ga masu bukata ta musamman.
Ina tunatar da duk wani zababbe da ke kan wata kujera ya tuna cewa da kuri’ar masu bukata ta musanmman ya samu kai wa ga wannan matsayi, don haka sai ya yi tunanin me zai iya yi musu a matsayinsu na wadanda suka zabe shi.
Ba zan manta da lokacin Gwamnan Kano Kanar Idris Garba ba, wanda ya tabbatar cewa a mai’aikatu da kamfanonin da ba na gwamnati ba dole sai an ware wani kaso ga masu bukata ta musamman kamar yadda aka yi tanadi a majalisar dinmin Duniya. To Idan har wanda ba ka zaba ba zai yi maka irin wanann tagomashin, to ina ga wanda ka zaba. Don haka na kalubalanci duk wani zabababen shugaba tun daga sama har kasa, su zauna su yi tunani mai suka yi wa masu bukata ta musamman. Ina kira da a samar da daidaito tsakanin masu bukata ta musamman da sauran jama’a ta kowace fuska.
Haka kuma ina kira ga sauran jama’a masu hannu da shuni da su shigo wajen karfafa gwiwar masu bukata ta musamman, musamman ta fuskar ilimi. Ba zan mance yadda wani attajiri lokacin muna karatu a Jami’ar Bayero ya bayar da makudan kudi don rabawa ga dalibai masu bukata ta musamman ba.
Haka kuma duk da cewa bara ba abu ne mai kyau ba, amma bai kamata a hana ta ba, bayan ba a samar wa mutum wani abu da zai rika yi don sama wa kansa abin kai wa bakin salati ba. Ita kanta barar ai tana nuna gazawar gwamnati ce a fili. A kasar nan babu kabilar da a cikinta babu masu bukata ta musamman, amma bahaushe ne kawai ke yin bara, saboda gwamnatinsa ba ta ba shi kulawar da ta dace.
Ina ganin sai mutum ya samu ilimi sannan cikin hikima zai fahimci me ya kamata ya yi a rayuwarsa, don haka masu bukata ta musamamn suna bukatar ilimi. Haka kuma wadand suke manya a samar musu wurin horarwa ta sana’a ta yadda za su dogara da kansu.
Title :
Makaho mai koyar da masu ido karatu
Description : Malam Yusha'u Ibrahim Malam Yusha’u Ibrahim kofar Waika, malami ne da ke koyar da masu ido a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi a K...
Rating :
5