Malam Muhammadu dantakwacco wani makaho ne da ke zaune a kauyen Tafki cikin gundumar Jabo a karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sakkwato. Wannan makahon yana da abubuwan al’ajabi da yake aiwatarwa. Aminiya ta zanta da shi kan rayuwarsa tare da neman fayyace gaskiyar batun da ake bazawa cewa akasarin abubbuwan da mai ido ke yi yana iya aiwatar da su. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ka fada mana sunanka da kuma bayaninka?
dantakwacco: Sunana Mahammadu Maigari, wanda ake yi wa lakabi da dantakwacco, a wannnan kauyen na Tafki nake rayuwata, yau kusan shekara 50 ina zaune a kauyen, makaho ne ni, amma ba da makantar aka haife ni ba, daga baya ne abin ya same ni, dayan idon ya rufe ne sakamakon ciyon Ado da na yi fama da shi ina yaro karami, dayan kuwa ya rufe ne sanadiyar Iska, watau Jinnu. A hakan na ci gaba da rayuwata har zuwa yau.” a cewar Dantakwacco.
Aminiya: An ce akwai abubuwa na al’ajabi da mutane ke fadin cewa kana yi, haka ne?
dantakacco: Gaskiya ni makaho ne kamar yadda na fada maka tun farko, kuma kai ka tabbatar da hakan, ban san adadin abin da mutane suka fada maka a kaina ba, da wannan nake fada maka ni dai zan fadi iya abin da na sani ina aikatawa wadanda masu gani da ido ne kadai aka san suna aiwatawa.
Ina tuka keke tsawon shekaru da suka wuce, kuma har yanzu ban daina zuwa inda na saba tafiya da keke ba, daga Tafki har zuwa Modo(tafiyar kilomita biyar,) kuma nakan yi tafiya a hannuna ba tare da samun wata matsala ta kaucewa daga kan titi ko fadawa rami ba, babu wani keke a kasar nan da bana iya hawa in yi tafiya, ya yadda idan ba ka san ni ba ba za ka ce ba makaho ne ke kan keken ba. Na yi noma sau biyu a rayuwata ta makanta, kuma wannan kacin rai ne ya haddasa aikuwar hakan.
A lokacin wata damina ce na kira wani matashin manomi muka yi jingar noma da shi na ba shi kudina, daga nan ya yi min batan-dabo, ganin kada in bari amfanin gona ya lalace kawai sai na tafi na yi noman da kaina, har sau biyun, kuma babu wata shuka da ta samu matsala. Da zarar na isa wurin shuka sai in zagaye ta da kasa in wuce.
Aminiya: Akwai wadansu kuma abubuwan da ke yi bayan wadannan?
dantakwacco: Nakan je daji da jakina, tun kafin na mallaki keken hawa, in saro itace in daure in dora masa zuwa gida, yanzu kuwa da keke nake tafiya in saro itacen in zo ina sayarwa da kuma amfanin gida, ko wannan rumfar da kake gani a bakin gidana ni ne na saro itacen daga daji kuma na kafa rumfar da kaina. Ba zan iya fadar adadin abin da na samu ba, amma a kullum nakan samu jikka biyar (N1000) ko kasa da haka daga kudin itacen da nake sayar wa jama’a.
Haka kuma ina zuwa dibar ruwa, don muna da rijiyoyi a wannan kauyen, sai dai a wurin wata rijiya daya ce tak nake dibar ruwa, domin ita kadai ce na amince da ita, ko dare ko rana nakan je in debo ruwa a rijiyar ba tare da wani abu ya taba faruwa gare ni ba.
Kuma duk abin da na mallaka idan har ya bata na je nemansa idan yana wurin da na je to zan gane abina, akuyata da jaki da kajina sun sha bacewa, da zarar na tafi kasuwa idan har an zo da su kasuwar wurin sayarwa idan na nemi damar in bincika aka amince to zan kamo nawa, kuma shi ne ba wata jayayya. Jakina ko cikin jakai dari aka sanya shi sai na fitar da shi. An sha gwada ni kan haka, baiwa ce kawai, da zarar na lallaba na taba nawa ina ganewa a jikina.
Aminiya: Ko ka taba samun tallafin gwamnati wanda ake ba nakasassu a jihar Sakkwato?
dantakwacco: Ba a taba ba ni wannan tallafin ba, kuma an kira mu Tambuwal aka dauki sunayenmu kamar da gaske, har yanzu shiru, sai dai mun samu labari gwamnati na fitar da kudinmu mu ne ake hanawa, mun ta zuwa wurin wadanda ke da alhakin biya har mun gaji, ba a taba ba ni ba. Ina kira ga gwamnati ta waiwaye mu.
Da Aminiya ta tuntubi Dagacin garin Tafki Malam Abubakar domin jin ta bakinsa kan wannan makahon sai ya ce, “Wannnan makahon a matsayin da yake a wurina, baiwarsa tana da yawa da ban al’ajabi, duk abin da ya fada maka mu shaida ne kan haka, don mun yi ta gwada shi da wadansu abubuwa wadanda muke ganin kamar ba haka ba ne amma ya aikata su yadda ko mai ido nan zai tsaya, gaskiya ni ban taba samun labarin makaho mai yin wadannan abubuwa da dantakwacco ke yi ba. Ga shi ko dan jagora ba ya da.
Daga farko lamurransa na daure mana kai, amma yanzu duk abin da ya yi ba zai ba mu mamaki ba, don da wuya ya yi kamar hawan keken da yake yi ya tafi inda yake so, don mun yi ta kokarin mu hana shi amma ya ki, ga shi Allah Ya tsare shi har yanzu babu abin da ya shafe shi.’’ A cewar Dagacin.
Title :
Makaho Mai Ayukan Irin Na masu Ido
Description : Malam Muhammadu dantakwacco wani makaho ne da ke zaune a kauyen Tafki cikin gundumar Jabo a karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sakkwato. Wa...
Rating :
5