Assalamu alaikum Wa Rahmatullahi wa barka tuhu. dafatan malam kana lafiya tare da iyanlan Allah ya albarkaci zuri'arka Ameen. Mallam Don Allah ina neman maganine ko kuma aban shawara mamana ne guda 1 yake fidda ruwa yellow haka kaman ruwan kabewa kuma wani lokacin yanamin ciwo har yana hanani sa BRA naje hospital anyi scanning sunce bakomai ma'ana banida matsala sai pain reliever kawai suka bani kuma bai dena ba ya kusa 5 years da fara fitan ruwan gashi bantaba haihuwa ba balle ince ko ruwan nono ne shine nakeson ataimakamin da magani ko shawara. Sakhallahu Khairan.
AMSA
********
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Ki nemi Garin Shammar, Garin Hulba, ganyen Jirjir. Ki hadasu waje guda ki rika dafawa kina shan ruwan tare da zuma. In sha Allahu Nonon zai dena ciwo, ruwan zai dena zuba kuma zai dawo da shape dinsa.
Ki samu Man zaitun ayi karatu acikinsa sannan ki rika shafawa ajikin Nonon. In sha Allahuzaki samu waraka da izinin Allah.
Dangane da rashin haihuwar kuma Ki samu Furen Albabunaj ki hada da ganyen Sazabu. (idan baki samu ganyen sazabun ba, kiyi amfani da fure. albabunaj din kadai). Ki rika dafawa kina sha kamar Tea.
Sannan ki rika yin matsi da Man Albabunaj din. Ki samu tafarnuwa ki sanya acikin gabanki kamar tsawon awa uku kullum. Sannan kije ki wanke da ruwan dumi.
In sha Allahu wannan zai bude miki mahaifarki, kuma zai kashe kwayoyin cutar da suke wajen. Zaki samu haihuwa da izinin Allah.
Kuma ki yawaita shan zuma duk lokacin da kike Haila. Wannan ma zai taimaka miki sosai da yardar Allah.
Allah yasa adace.
WALLAHU A'ALAM.