Ma'aikatar Shari'a ta Najeriya ta bukaci kotun kula da da'ar ma'aikata ta ba da sammacin kama shugaban majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki.
Mataimakin darakta a ofishin Ministan Shari'a na kasar, Mr M.S. Hassan, ya bukaci a dauki matakin ne bayan, a cewar sa, Saraki ya ki gurfana a gaban kotun kula da da'ar ma'aikata domin kare kan sa daga zargin yin karya wajen bayyana kadarorinsa.
Kotun da'ar ma'aikatan ta bukaci Mr Saraki ya gurfana a gaban ta a safiyar juma'a, sai dai a madadin haka lauyoyinsa sun bayyana a kotun inda suka gabatar da wata wasika daga wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Babbar kotun ta Tarayya dai ta bukaci shugabannin hukumar kula da da'ar ma'aikata da kotun kula da da'ar ma'aikata da Mr M.S. Hassan su gurfana a gaban ta domin su gamsar da ita a kan dalilan da za su sa a ci gaba da yi masa shari'a.
Ita dai ma'aikatar shari'ar ta ce babu wata kotu da ke da hurumin hana Mr Saraki gurfana a gaban kotun da'ar ma'aikatan, ko kuma bai wa kotun ta musamman sammacin gurfana a gaban ta, tana mai cewa shugaban majalisar dattawan yana yunkurin gujewa shari'a ne kawai.
Lauyoyin da ke kare shugaban Majalisar Dattawan dai sun ce a bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki, bai halatta ba a gurfanar da mutum a gaban kotun da'ar ma'aikatan sai da izinin Antoni Janar na Tarayya (Ministan Shari'a), mukamin da a yanzu babu mai rike da shi.
Hukumar da'ar ma'aikata ta gurfanar da shugaban majalisar dattawan ne a gaban kotun da'ar ma'aikata bisa wasu zargi 13 na yin karya wajen bayyana kaddarorinsa, zargin da Bukola Saraki ya musanta ya na mai cewar bai aikata wani abu da ba daidai ba.
Title :
Ma'aikatar Shari'a na neman a kama Saraki
Description : Ma'aikatar Shari'a ta Najeriya ta bukaci kotun kula da da'ar ma'aikata ta ba da sammacin kama shugaban majalisar dattawan ka...
Rating :
5