Robert Lewandowski ya sake kafa tarihi a Bayern
Munich, bayan da ya ci kwallaye a karawar da Munich ta
doke Mainz da ci 3-0 a gasar Bundesliga.
Lewandowski ne ya ci kwallaye biyu a wasan da hakan ya
sa ya zura kwallaye 100 jumulla daga wasanni 168 da ya
yi a gasar, kuma dan kwallon da ba dan kasar Jamus ba
da ya yi hakan.
Haka kuma dan wasan ya zamo na biyu da ya ci kwallaye
10 a gasar, bayan da aka buga wasanni bakwai. Gerd
Muller ne ya fara kafa tarihin yin hakan.
A tsakiyar makon da ya gabata ne Robert Lewandowski
dan kasar Poland mai shekaru 27 ya ci kwallaye biyar a
cikin minti tara a karawar da Munich ta ci Wolfsburg a
gasar ta Bundesliga.
Title :
LEWANDOWSKI ya sake kafa tarihi
Description : Robert Lewandowski ya sake kafa tarihi a Bayern Munich, bayan da ya ci kwallaye a karawar da Munich ta doke Mainz da ci 3-0 a gasar Bundes...
Rating :
5