Wadannan Sharuda sai sun cika, sannan layyar zata zama karbabbiya. Gasu nan kamar haka:
1. NIYYAH: ita ce sharadi na farko. Wajibi ne mutum ya kyautata niyyarsa yayin da zai yi yankan ya yanka da nufin neman kusanci da Allah (SWT).
2. ABINDA ZA'A YANKA : Dole ne abinda za'a yanka ya zamto daga nau'in dabbobin nan guda hudu :
* Tunkiya ko rago.
* Bunsuru ko Akuya.
* Saniya ko Bijimi.
* Rakumi ko Taguwa.
Bai halatta ayi layya da wani abinda ba wadannan ba.
3. LAFIYAR DABBA : Wajibi ne ya zamto dabbar ta kubuta daga manyan aibubbuka. Misali ba'a yi da dabbar da ta zamo:
* Makauniya ko Mai ido daya, wacce Makantar ta abayyane take.
* Ramammiya, Marar lafiya wacce jinyarta ta bayyana afili.
* Gurguwa wacce gurguntakar ta bayyana afili.
* Karyayya wacce Qafarta ta karye, kuma bata warke ba. ko wacce mafi yawan kunnenta ayanke yake.
4. RANAKUN YANKAN : Wajibi ne ayanka layyar acikin ranar sallah ko kuma ranaku biyun da suke biye da ita. Idan aka yanka awata ranar daban, to bai zama layya ba.
5. LOKACIN YANKAN : Wajibi ne ya zama anyi yankan ne bayan saukowa daga sallar Eidi, kuma bayan Sarkin garin ko Shugaban mutanen garin ya yanka nasa.
Idan aka yanka kafin Sallar Eidi to bai zama layya karbabbiya.
Saboda hadisin da Ma'aiki (saww) yake cewa: "DUK WANDA YAYI YANKA KAFIN SALLAR EIDI TO YA YANKA NE KAWAI DOMIN KANSA $WATO BA DON ALLAH BA KENAN). AMMA WANDA YA YANKA BAYAN SALLAH, TO YA CIKA YANKANSA KUMA YA DACE DA SUNNAR MUSULMAI".
Title :
Layya Tana Da Sharadan Ingaci Gudu Biyar
Description : Wadannan Sharuda sai sun cika, sannan layyar zata zama karbabbiya. Gasu nan kamar haka: 1. NIYYAH: ita ce sharadi na farko. Wajibi ne mutum...
Rating :
5