BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Tsira da aminci su tabbata bisa Mafi girman matsayi acikin dukkan halittun Allah, Shugabanmu Annabi Muhammadu Tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahbbansa zababbu.
Yau in sha Allahu muna tare da daliban ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3) kuma zamu gudanar da darasinmu akan tarihin wasu Qabilu ne wadanda yanzu haka suna nan da ransu. Amma ba zasu bayyana ba, sai akarshen zamani. Sunansu YAJOOJU WA MAJOOJU.
Acikin Alqur'ani, Allah ya bamu labarin tafiye tafiyen da Sarki Dhul-Qarnaini yayi.
Acikin tafiye tafiyen nasa, yaje wajen da rana take faduwa, sannan yaje yaje mahudarta.
Sannan a tafiyarsa ta uku kuma yaje chan karshen duniya, kusa da bangon duniya.
Achan din ne mutanen wajen suka kawo masa Qara. Suka ce masa :
"YA KAI DHUL QARNAINI, HAKIKA YAJOOJU DA MAAJOOJU MASU 'BARNA NE ADORON QASA. SHIN KO ZAMU SANYA MAKA WANI HARAJI (WANDA ZAMU BAKA) DOMIN KA SANYA WATA KATANGA ATSAKANINMU DA TSAKANINSU?".
Shi kuma sai yace "ABINDA UBANGIJINA YA BANI, SHINE YAFI ALKHAIRI. KU DAI KAWAI KU TAIMAKENI DA QARFI (KARFIN JAMA'A) ZAN SANYA WATA KATANGA MAI QARFI TSAKANINKU DA TSAKANINSU".
Daga nan Dhul-Qarnaini ya kama aiki, ya gina wata Katafariyar katanga ta Qarfe da dalma, wacce tafi Qarfin wadannan mutanen su haurata.
SHIN SU WANENE YAJOOJU WA MAJOOJU??
Bari mu leka cikin litattafan Tafseeri da hadisan Manzon Allah (saww) domin mu binciko labarinsu.
Al Imam Alqurtubiy (rah) daya daga cikin jerin Manyan Malaman tafseeri, yace "An samo hadisai da labarai dangane da fitowarsu da kuma siffofinsu. Kuma cewa suna daga cikin 'ya'yan YAFITHU ne.
Sayyiduna Abu Hurairah (rta) ya ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"An haifa ma Annabi Nuhu ('ya'ya guda uku) SAAMU, da HAAMU, da YAFITHU.
Shi samu shine ya haifi Larabawa da Mutanen Farisa (Iran kenan) da kuma mutanen Ruum (turawa kenan). Kuma akwai alkhairi acikinsu.
Shi kuma YAFITHU shine ya haifi YAAJOOJ da MAJOOJU da Turkawa da mutanen Saqalib, amma babu alkhairi acikinsu.
Shi kuma HAAMU shine ya haifi Qibtawa (mutanen Misra) Da Barbar (berbers, wasu mutanen daji ne, masu tsananin Yaki) da kuma Bakaken fata".
Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) ya riluwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"(Su Yajooju wa Majooju) Mutum guda daga cikinsu ba zai mutu ba, har sai bayan ya haifi 'Ya'ya Maza guda dubu daga cikin tsatsonsa.
Imamul Qushairiy ya ambato Abu Sa'eed Alkhudriy yana cewa "SU QABILU ASHIRIN DA BIYAR NE ABAYAN SU YAJUJU WA MAJUJU. MUTUM GUDA DAGA CIKINSU DA KUMA CIKIN YAJOOJU WA MAJOOJU BA ZAI MUTU BA, HAR SAI NAMIJI GUDA DUBU SUN FITA DAGA CIKIN TSATSONSA.
Lallai bisa ga wadannan hadisan zamu iya cewa indai kowanne mutum guda daga cikinsu yana haifar mutum dubu, to lallai ba Qaramin yawa ne dasu ba.
Abdullahi bn Mas'ud (ra) yace: "Na tambayi Manzon Allah (saww) dangane da Yajooju wa Majooju, Sai shi Mai tsira da aminci) yake cewa :
"SU YAJUJU WA MAJOOJU AL'UMMATAI NE GUDA BIYU. (WATO YAJOOJU DABAN, MAJOOJU MA DABAN).
Kowacce Al'ummah daga cikinsu tana Qunshe da wasu Al'ummatai (ko Qabilu) guda dubu dari hudu (400,000 tribes). Kuma kowacce al-ummah babu wanda yasan iyakar yawansu sai dai Allah".
"KUMA MUTUM GUDA DAGA CIKINSU BA ZAI MUTU BA, HAR SAI BAYAN AN HAIFA MASA MAZAJE GUDA DUBU DAGA CIKIN TSATSONSA, KOWANNENSU YANA DAUKE DA KAYAN YAQI".
Sai wani Sahabi yace "Ya Rasulallahi, Siffanta mana su mana!".
Sai yace : "SU NAU'I UKU NE (KAMANNIN HALITTARSU).
1. AKWAI WADANDA SUKE (DA TSAWO) MISALIN BISHIYAR NAN TA URZU. WATA BISHIYA CE NAI TSAWON ZIRA'I 'DARI DA ASHIRIN.
2. SAI KUMA WASU NAU'I WADANDA TSAYINSU DA KAURINSU DUK 'DAYA NE - WATO ZIRA'I GUDA. (TSAWONSU ZIRA'I DAYA, KAURINSU MA HAKA).
3. SAI KUMA WANI NAU'IN WADANDA SUKE (DA MANYAN KUNNUWA) SUNA SHIMFIDA KUNNE 'DAYA SUYI KAFITA DASHI.
'DAYA KUNNEN NASU KUMA SUYI MAYAFI DASHI".
BA ZASU WUCE TA KUSA DA WATA GIWA KO NAMAN DAJI, KO ALADE (AL-HANZIR) BA, FACHE SAI SUN CINYESHI.
KUMA DUK WANDA YA MUTU DAGA CIKINSU MA, CINYESHI SUKE YI (WATO SUNA CIN NAMAN 'YAN UWANSU).
NA GABANSU SUNA KASAR SHAM, 'YAN BAYANSU KUMA SUNA KHUR KHURASAN (WATO AFGHANISTAN).
ZASU SHANYE KOGUNAN GABASHIN DUNIYA, KUMA ZASU SHANYE BUHAIRATUT TABRIYYAH (WANI KOGI NE A KASAR FARISA).
AMMA ALLAH ZAI KANGESU DAGA SHIGA GARIN MAKKAH DA MADINA DA BAITUL MAQDIS".
Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (ra) yace: "akwai wasu nau'i daga cikinsu wadanda tsawonsu kamar kamu guda ne (wato tsawon yatsa guda biyu).
Suna da farata (farce) da kuma Hakora irin na Zakoki. Da jiki irin na dabbobi, suna kuka irin na Kuraye, kuma suba taruwa kamar yadda tattabaru sukeyi.
Suna da gashi duk jikinsu, wanda yake karesu daga Sanyi da zafi.
Suna da manyan kunnuwa guda biyu. Daya kunnen na gashi ne. Suna fakewa daga Sanyi acikinsa. 'daya kunnen kuma na fata ne. Dashi suke fakewa alokacin zafi.
Suna tonon wannan katangar, sai sun kusan tureshi sai kuma Allah ya mayar dashi kamar yadda yake.
Sai sunce gobe zamu tureshi "IN SHA ALLAHU TA'ALA". Sannan zasu tureshi, su fito (zuwa cikin duniya).
Mutane zasu tsere daga garesu acikin manyan katangu da benaye (saboda suna kashewa duk mutanen da suka kama, sannan su cinye namansa 'danye).
Daga nan sai su rika harba kibiyoyinsu zuwa sararin samaniya, sai adawo musu da kibiyoyin chakude da jini.
Daga nan sai Allah ya sanya musu wata chuta (mai kamar tsotsa) a wuyansu, ya hallakar dasu.
Manzon Allah (saww) yace "NA RANTSE DA WANDA NUMFASHINA KE HANNUNSA, DABBOBIN DA SUKE DORON QASA SAI SUN QOSHI SUNYI KITSE SOSAI DAGA CIN NAMAN YAJOOJU WA MAJOOJU DA KUMA JININSU
Imamu Ahmad da Tirmiziy, da Ibnu Maajah ne suka ruwaitoshi.
Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) yaji Manzon Allah (saww) yana cewa:
"Za'a bude ma Yajooju wa Majooju Qofa su shigo cikin duniya, kamar yadda Allah ya fada, "SUNA TAFIYA DA SAURI TA CIKIN DUKKAN SASANNI".
Mutane zasu firgita su gudu daga garesu, zasu fake daga garesu acikin katangu da birane. Kuma zasu taho da dabbobinsu ma tare dasu.
Mutanen Yajooju wa Majooju din zasu yi yawo adoron Qasa, zasu shanye duk ruwan dake doron Qasa. Wani daga cikinsu zai wuce ta kusa da wani kogi, sai yace "Da chan kuwa, akwai ruwa anan wajen".
Bayan kowanne mutum ya riga ya buya daga garesu, sai wani daga cikin YAJOOJU WA MAJOOJU yace : "Wadannan duk Mazaunan doron Qasa ne, mun gama dasu. Saura yanzu mazauna cikin Sammai".
Sai wani daga cikinsu ya harba kibiyarsa zuwa sama, sai adawo masa da ita, tana jike da jini. Suna cikin wannan halin sai Allah ya turo musu da wata irin chuta awuyansu, kamar tsutsotsin nan na Aljaraad zasu kama wuyansu. Zasu mutu, ko motsinsu ba Za'a ji ba.
(Imamu Ahmad ne ya ruwaito).
Awata ruwayar kuma, Annabi Eisa (as) shine zai yi addu'a sai Allah ya turo da Mala'iku suzo su kawar da Gawarwakin YAJUJU WA MAJUJU din, bayan sun cika duniya da warinsu.
Anan zamu tsaya sai a karatu na gaba. In sha Allahu zamu dauko wani batun mu tattauna akai.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3).