An kawo hikaya (labari) cewa akwai wani sarki
cikin mutane da suka gabata. Yana da wani
Bafade a fadansa, wanda duk abinda ya faru
acikin fadan sai sarkin ya tambaye shisai yace
ma Sarki "Yana fata alkhari ne" kullun idan aka yi
abu haka ya ke ce wa.
Sai wata rana aka ce Sarkin ya samu ciwo a
hannunsa sanadiyar yana so ya yanka wani abu
da wuka. Sai bafaden nan ya ce ma shi:"Ina fata
Alkhari ne" sai abun ya ba sarkin haushi, sai ya
ce ma bafaden: Komai aka yi saika ce alkhairi ne,
har da ciwon da naji? ..
Sai sarkin ya bada umurni cewa a kulle shi a
cikinkurkuku.
Sai wata rana sarkin ya ce yana so yayi tafiya
tare da fadawansa, Sai su kataho akan dawaki,
suna cikin tafiya sai su ka isa wani gari, wanda
mutanen garin mushrikai ne masu bautan
gumaka. Kuma a tsarin su, sukan kama mutane
da su ke wucewa ta hanyan garin su,su kashe su,
su je su nemi albarkan gumakan su da gawan
(sacrifice).
Sai su ka kama sarkin da fadawansa, Su ka ajiye
su, Sai aka ce aje a kawo su a rinka yayyanka su,
amma suna da sharadi na cewa, duk wanda za a
yanka sai an tabbatar ba yi da ciwo a jikinsa, Sai
su ka dudduba su, su ka gano babu wanda ke da
ciwo sai sarkin nan da ya yanke a hannunsa, sai
suka sake shi ba su yanka shi ba.
Da komawar sa garin sa, sai ya ce a saki wannan
Bafaden da duk abinda ya faru sai yace ALKHAIRI
NE. Sai sarkin ya ba shi labarin abin da ya same
shi. Sai sarkin ya gaskanta cewa: "Duk abinda ya
faru ga mutum ko yana so ko baya so alkhari ne
gare shi".