Wata kungiya mai suna Yoruba Youth Alliance na gargadin Shugaba Muhammadu Buhari akan tugumar da ake yi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki inda suka kira hakan “Bin diddiki.” Shugaban Kungiyar, Mista Jackson Ojo ya bayyana cewa wannan ba yaki akan rashawa bane, bin diddiki ne.
Yace: “Akwai jita jita cewa wannan na faruwa ne saboda zaman da saraki yayi shugaban Majalisar Dattawa duk da cewa wasu manyan APC ba haka suka so ba. Duka duniya na ganin abunda ke faruwa. Muna zargin cewa akwai wanda ke harzuga abun domin ya bata saraki don ya zama Shugaban Majalisar Dattawa duka da manyan APC basu so haka ba.
“Abunda nike so shine, abi a hanakali akan wannan lamari. Domin kuwa idan ba’ayi taka tsantsan ba, wannan zaya iya dawowa akan jam’iyyar sannan kuma ya maida yaki da rashawar da shugaba Buhari yake yi wasa.
“Saraki bai fi karfin doka ba, amma abi doka wajen ganin anyi komai.” Jaridar Punch ta ruwaito.
Ojo ya kara jadada cewa ana yin amfani da Code of Conduct Bureau (CCB) ne domin a musguna ma Saraki.
Yace: “Ina yin Allah wadai da abunda ke faruwa ga Saraki a hannun CCB. Duk da cewa ya kamata suyi aikin su ba tare da jin tsro ba ko alfarma, amma ya kamata ayi shi cikin tsarin gaskiya.
“Saraki ya bayyana kaddarorin shi a 2003 lokacinda ya zama gwamna, da kuma 2007, da kuma lokacin daya zama Sanata a 2011. Duk lokaci ba a ce komai ba sai yanzu shekaru 12 sannan.”
Ojo ya bukaci a hukunta Saraki idan an kama shi da rashin gaskiya. Amma ya bukaci hukamar tayi komai cikin tsari domin kada a zargeta da zama karen farautar APC.
Title :
Kungiyar Yarrabawa Ta Gargadi Buhari Akan Saraki
Description : Wata kungiya mai suna Yoruba Youth Alliance na gargadin Shugaba Muhammadu Buhari akan tugumar da ake yi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Bukol...
Rating :
5