Huzaifah Ibnul Yamaan (ra) yace:
"FARKON ABINDA ZAKU FARA RASAWA DAGA CIKIN LAMARIN ADDININKU, SHINE TSORON ALLAH (ACIKIN SALLAH).
KUMA QARSHEN ABINDA ZAKU RASA DAGA CIKIN ADDININKU SHINE SALLAH.
KUMA DA YAWA DAGA CIKIN MASU SALLAH BABU ALKHAIRI CIKINSU.
LOKACI YA KUSA WANDA JAMA'A MAAU YAWA ZASU SHIGA MASALLACI AMMA BA ZAKA GA MAI TSORON ALLAH ACIKINSU BA".
ZAUREN FIQHU : Wannan Sahabin da ya fadi wannan maganar, yana daga cikin Manyan Sahabbai yardaddu awajen Allah da Manzonsa (saww).
Kuma Manzo (saww) ya kebanceshi da maganganu na sirri irin wadanda bai gaya ma kowa ba. Don haka ake kiransa da suna "Ma'abocin Sirrin Manzon Allah (saww)".
Bisa dukkan alamu wannan zamanin da muke ciki shine wannan lokacin da ake nufi. Domin kuwa yanzu wasu Malaman sun mayar da Masallatai kamar kasuwanninsu wajen neman abin duniya.
Sun fi damuwa da kyautata Muryarsu fiye da kyautata sallarsu. Kai daga jin muryoyin WASU malaman, da kuma irin yadda suke gudanar da lamarin sallarsu ka san zai yi wuya asamu cikakken tsoron Allah anan.
Wannan shine zamanin da Mutum zai shiga wajen sallah amma yana tsoron 'barayi zasu iya sace masa takalmansa ko abin hawansa.
Na san cewa ko acikin zauren nan ba za'a rasa wadanda aka taba yi musu satar takalmi ko keke ko babur ko Motarau ko ta abokinsu a Masallaci ba!!!
Awanu labarin ma ance akwai masu yin YANKAN ALJIHU a Masallacin Ka'abah!!! Dakin Allah mai tsarki!!!
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!