Alkalin Babbar Kotun Nijeriya da ke Abuja, Ademola Adeniyi, ya bayar da belin tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkar tsaro, Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya).
Alkalin ya bayar da belin Dasuki ne bisa “lura da kimar sa” ta kasancewa daya daga cikin mutanen da suka bautawa Nijeriya.
Gabanin bayar da belin nasa, lauyan gwamnatin tarayya, Mohammed Diri, ya shaida wa kotun cewa sun gurfanar da shi a gaban ta ne bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
A cewar sa, hukumar tsaron farin-kaya ta kasar ta je gidan Kanar Dasuki a watan jiya, inda ta same shi da makamai.
Ya kara da cewa hakan zai iya sanya wa a daure shi a karkashin dokokin Nijeriya.
Sai dai da aka karanta wa Kanar Dasuki zargin da ake yi masa, ya musanta.
Lauyansa, J.B. Daudu, ya bukaci kotun ta bayar da belinsa, kuma masu shigar da kara ba su nuna kin amincewa da bukatarsa ba.
Alkalin ya bukaci bangarorin biyu su gurfana a gaban sa ranar 26 da 27 ga watan Satumba domin ci gaba da shari’a.
Sai dai ya bukaci a kwace fasfo din Kanar Dasuki, a ajiye a kotun domin kada ya fice daga kasar.
Kanar Dasuki shi ne babban jami’in gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da aka gurfanar a gaban kotu ya zuwa yanzu.
Idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar daurin shekaru goma a gidan yari.
Title :
Kotu Ta Bayar Da Belin Sambo Dasuki
Description : Alkalin Babbar Kotun Nijeriya da ke Abuja, Ademola Adeniyi, ya bayar da belin tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkar tsaro, K...
Rating :
5