Manzon Allah (saww) yayi saye da sayarwa, amma bayan Allah ya girmamashi da Manzanci sayensa yafi sayarwarsa yawa.
Hakanan bayan yayi hijira, bai cika sayar da wani abu ba, sai dai awasu 'yan lokuta, bisa wasu dalilai.
Amma sayen abu shi yafi yawa gareshi. Domin kuwa Tarihi ya nuna cewa kafin Annabta Manzon Allah (saww) yayi kiwon dabbobi, kuma yayi ma Nana Khadijah fatauci da dukiyarta zuwa Birnin Sham. Har sai da dukiyarta tayi albarka ta ninninka yadda take.
Kasancewar Noma da kiwo da Kasuwanci duk sana'o'in Annabawa da Manzanni ne (alaihimus Salam) shi ya sanya ma wadannan sana'o'in albarka, duk garin da kaje aduniya sai ka samu masu yinsu. Kuma sai kaga cewa sune mutane suka fi bukatuwa zuwa garesu.
Ya Allah yi salati da amincinka gareshi da iyalan gidan gwargwadon dawwamar Mulkinka mai tsarki.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3)