Shugaban Kasar Faransa Farancois Holande ya tabbatar a
yau Lahadi cewa kasar sa ta kai hari a wani sansanin
horasda ‘yan ta’adan (IS) a kasar Syria. Mr Hollande ya
bayyana hakan ne a birnin New York inda yake halartar
babban taro MDD. Bayan wannan harin da jiragen yakin
kasar sa suka kai a sansanin dake kusa da Deir Ezzor
dake gabashin Syria, Hollande ya kara da cewa kasar sa
zata kara daukan wasu matakai nan gaba domin ganin
bayan ‘yan ta’adan, wanda daga kasar ta Syria ne suke
shirye kai hare haren su a kasar Faransa. Hakan dai na
zuwa ‘yan kwanaki kalilan bayanda Farasan ta aike
jiragen leken asirin ta a kasar ta Syria, kuma ta ce tayi
hakan ne bisa ‘yancin da take dashi na hadin guiwa da
abukan kawancenta dake gabas ta tsakkiya.
Title :
Kasar Faransa Ta Kai
Hari Kan Sansanin ‘yan
Ta’adan (IS) A Syria
Description : Shugaban Kasar Faransa Farancois Holande ya tabbatar a yau Lahadi cewa kasar sa ta kai hari a wani sansanin horasda ‘yan ta’adan (IS) a ka...
Rating :
5