Assalam alaikum. Don Allah a taimakamin da addu'a, Allah yayiwa mijina rasuwa, duk da na yarda da gaskiya gaskiya ce amma xuciya ta ta kasa samun natsuwa, tunani shine abincina. na kuma tabbatar ba zai dawo ba. ba damar inga wata na zancen mijinta. ko kuma inga wata da miji, sai in dinga jin ba'a kyauta min ba, har in dinga raya cewa mijin kowa ma ya mutu a huta. don Allah a taimaka min da addu'a, da kuma nasiha ko zuciyata zata sami natsuwa, wallahi malam saboda kuka har na fara rashin hangen nesa, don Allah a taya ni da addu'a.
(daga wata Baiwar Allah).
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh. Da farko dai muna tayaki addu'ar Allah ya jikan Mijinki, Allah ya sadashi da rahama.
Sannan abinda ya kamata ki lura dashi shine: KI DUBI GIRMAN UBANGIJINKI da Gwanintarsa acikin halittunsa da hikimarsa acikin yadda yake jujjuya lamarin bayinsa yadda yaso.
Ki sani cewa Ubangiji yana da wata hikima wacce ya 'boye acikin dukkan abinda ya Qaddara ma bayinsa. Watakil kiga hikimar tunda wuri. watakil kuma ba zaki ganta ba, sai daga baya.
Ita rayuwa da mutuwa, duk Allah ya haliccesu ne domin jarrabawa ga bayinsa. Domin ya ware wadanda zasu fi kyautata ayyukansu.
Ki sani cewa kowanne mutum tun yana cikin mahaifiyarsa Allah ya riga ya rubuta masa adadin shekaru da kwanaki da Mintunan da zai yi aduniya. Kuma ya Qaddara masa dukkan abinda zai samu, da kuma abinda zai sameshi. Babu chanzawa, babu Qari, babu ragewa.
Ko kin san cewa Annabawa sune mutanen da Allah yafi kauna, su suka fi kowa kusanci dashi? To amma akwai Annabawan da suka rasu tun suna Samari. Ko auren fari basuyi ba. Wasunsu ma kashesu akayi.
Misali kamar Annabi Yahya bn Zakariyya (as). Sannan ga Annabi Eisa (as) shi bai mutu ba, amma daukeshi Allah yayi zuwa gareshi.
Sannan ki dubi Shugaban Halittar Allah baku daya, Annabi Muhammadu (saww) yadda ya taso acikin Maraici. Mahaifinsa ya rasu tun ba'a haifeshi ba. Mahaifiyarsa ta rasu yana da shekaru 6 aduniya. Kakansa ya rasu yana da shekaru 8 aduniya.
Kuma 'Ya'yansa Shida ne suka rasu ahannunsa. Matarsa ma wacce yafi so itama ahannunsa ta rasu. Sannan ga jikanunsa da dama duk sun rasu.
Ki sani cewa dukkan abinda Allah ya bayar, to nasa ne... Wanda ya karba dinma duk nasa ne. Don haka kiyi hakuri ki bar ma Allah lamarinsa. Kiyi fatan Allah ya baki hakurin jurewa, sannan ki roki Allah ya raya muku 'ya'yan da kuka haifa bisa tafarki madaidaici.
Ki sani cewa Allah ne ya hadaki da Mijin naki. Kuma duk kirkinsa da soyayyar da yake nuna miki, to Allah yana da wasu bayin wadanda suka fishi. Don haka idan kikayi hakuri Allah zai chanza miki da wani mutumin kirkin. wanda hankalinki zai kwanta dashi.
Ummu Salamah (ra) lokacin da Mijinta ya rasu, tayi bakin ciki sosai. Amma tayi hakuri tayi addu'a. Amma tana tunanin kamar ba zata samu kamarsa ba, saboda irin soyayyar da yake nuna mata.
Tana nan Sai Manzon Allah (saww) ya aika mata cewa yana son zai aureta. Kin ga kenan ta samu wanda ya zarce mijin nata fiye da sau Dubu.
Kema idan kikayi hakuri Allah zai miki wata babbar kyautar.
Ina baki shawara cewa ki dena wani mugun tunani. wannan duk aikin shaitan ne. yana so ya hanaki samun ladan hajurin ne. Don haka ki yawaita Zikirin Allah da Karatun Alqur'ani da Salatin Annabi (saww).
Ki sani cewa IMANI DA QADDARA TA ALKHAIRI KO SHARRI shine mafi wuya daga cikin ginshikan Imani. Rashin yinsa zai iya janyo miki rugujewar imaninki.
WALLAHU A'ALAM.