Hare-haren wuce gona da irin kasar Saudiyya kan garin Ibb da ke kudancin kasar Yeman sun yi sanadiyyar shahadar mutane akalla 12 tare da jikkata wasu 54 na daban.
Majiyar tsaron Yamen ta sanar da cewa: Jiragen saman yakin Masarautar Saudiyya sun kai hare-haren wuce gona da iri da makamai masu linzami kan gidajen mutane a tsakiyar garin Yarim da ke lardin Ibb a jiya Litinin, inda suka yi sanadiyyar kashe mutane akalla 12 da suka hada da mata da kananan yara gami da jikkata wasu 54 na daban.
Har ila yau hare-haren sun yi sanadiyyar rusa gida masu yawa lamarin da ya tilastawa jama’ar yankin barin muhallinsu. Mahukuntan Saudiyya da sauran kasashen Larabawa da suke goya musu baya a yaki kan kasar Yemen sun kara karfafa yawan sojojinsu tare da jibge tarin makaman yaki da nufin bullo da wani sabon salon murkushe al’ummar Yemen tun bayan halakar sojojin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa 45 da na Saudiyya 10 gami da Bahrain 5 a garin Ma’arib na kasar Yemen a kwanakin baya.
Title :
Jiragen Saman Yakin Saudiyya Suna Ci Gaba Da Kashe Al'ummar Yemen
Description : Hare-haren wuce gona da irin kasar Saudiyya kan garin Ibb da ke kudancin kasar Yeman sun yi sanadiyyar shahadar mutane akalla 12 tare da j...
Rating :
5