Shaidun gani da ido sun bayyana cewa,jiragen sama na Isra'ila sun kai hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na Gaza da suka hada da; filin jirgin saman ma'aikatar harkokin cikin gida ta Falasdin da ke a Assudaniye.
Haka zalika, jiragen na Isra'ila sun kuma kai hari gundumar Bait Lahiye da kuma sansanin sojin Hamas na Izzeddin Al-Kassim da ke kudancin Gaza.
Babu wani da aka kashe ko jikkata sakamakon hare-haren, amma kuma an lalata gine-gine da dama.
An bayyana cewa, har yanzu jiragen na Isra'ila na ci gaba da shawagi a sararin samaniyar Gaza.
A baya dai sojin Isra'ila sun fitar da wata sanarwa cewa, sun tare wani makamin roka da aka jefa musu daga yammacin gabar kogin Jordan.
Title :
Jiragen saman Isra'ila sun kai hare-hare a Gaza
Description : Shaidun gani da ido sun bayyana cewa,jiragen sama na Isra'ila sun kai hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na Gaza da suka hada da; f...
Rating :
5