Kasashen nahiyar Turai musamman Jamus da Ostiriya sun fitar da sababbin matakai na dakile yawaitar kwararar 'yan gudun hijira da bakin haure cikin kasashensu.
Cikin makwanni biyun da suka gabata ne dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da cewa kofa a bude take ga duk wani dan gudun hijirar Siriya da ke son shigowa Jamus da mafi yawansu ke biyo wa ta kasar Ostiriya da Hangari a kokarin da suke na karasowa Jamus din. Merkel dai ta yi hakan ne ba tare da yin shawara da sauran takwarorinta na kasashen Turai ba musamman mambobin kungiyar Tarayyar Turai EU, kana matakin nata ya saba da yarjejeniyar Dublin da aka amince da ita a kan bakin haure da 'yan gudun hjira. Hakan dai ya janyo mata suka daga cikin gida da waje, misali abokiyar tagwaitakar jam'iyyarta ta CDU wato CSU a nan Jamus ta nuna adawarta da matakin na Merkel. Sai dai za a iya cewa Jamus din ta yi amanta ta lashe domin kuwa a karshen mako mahukuntan kasar sun sanar da daukar sababbin matakai na gudanar da bincike ga bakin haure da 'yan gudun hijirar da ke son shigowa Jamus wadanda ke biyowa ta kan iyakar kasar da Ostiriya.
Jamus ta yi amai ta lashe
Da yake kare wannan matakin da kasarsa ta dauka ministan harkokin kasashen ketare na Jamus din Frank-Walter Steinmeier ya ce yana mai alfaharin cewa kasarsa na da ga cikin kasashe kalilan da suka yi wa 'yan gudun hijirar maraba sai dai hakan baya nufin za su bar abubuwa su ci gaba da tafiya ba kula.
Ya ce: "Dole ne mu amince cewa a yanzu babu niyyar hadin kai tsakanin kasashen Turai kan batun 'yan gudun hijira. Muna nan kan bakanmu na tallafawa 'yan gudun hijirar kuma za mu ci gaba, sai dai dole ne mu tabbatar da cewa mun yi komai bisa ka'ida. Mun dakatar da jigilar jiragen kasa na daukar fasinja na tsahon sa'oi 12 kuma bamu rufe kan iyakokinmu ba, sai dai mun fitar da wani tsari. A baya babu wani jami'i da ke lura da wanda ke tsallako kan iyaka zuwa cikin kasarmu, yanzu kuwa akwai wannan tanadi sai dai hakan baya nufin mun rufe kan iyakokinmu baki daya."
Kasashen EU na koyi da Jamus
Tuni dai kasar Ostiriya da itama ta bude wa 'yan gudun hijirar kan iyakokinta ta bi sahun Jamus kana kasar Slovakia ma ta bi sahu wajen daukar kwararan mataki a nata kan iyakar domin rage kwararar bakin haure da 'yan gudun hijirar. A yayin wani taron manema labarai da shugaban gwamnati na Ostiriya da mataimakinsa suka gudanar sun jaddada cewa za su dauki matakin ne domin kariya ba domin musgunawa wani ba. A jawabinsa mataimakin shugaban gwamnatin Ostiriyan Reinhold Mitterlehner cewa ya yi:
"A ganina kuma na fada tun da farko duk abin da EU ta tsara da yarjejeniyar Dublin ta biyu ko ta uku da ma sauran matakai da za ta dauka a nan gaba basu da amfani, domin kuwa duk matakan na neman ba wa 'yan gudun hijira damar shigowa ta halastacciyar hanya ne abin da a yanzu babu ma batunsa kwata-kwata. A dangane da haka a wannan yanayi na gaggawa tilas ne mu dauki irin wadannan matakai."
Tuni dai ita ma kasar Hangari ta dauki matakin toshe kan iyakarta da Sabiya ta hanyar tura jami'an tsaro kan iyakar kasashen biyu domin dakile kwararowar 'yan gudun hijirar da bakin haure. Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNCHR) dai ta nuna damuwarta dangane da matakin da kasar Hangari din ta dauka. Ministocin cikin gidan na kasashen kungiyar EU na ci gaba da tattauna yadda za a bullowa batun raba dai-dai na 'yan gudun hijira da suka shigo Turai.
Title :
Jamus ta yi amai ta lashe dangane da batun 'yan gudun hijira
Description : Kasashen nahiyar Turai musamman Jamus da Ostiriya sun fitar da sababbin matakai na dakile yawaitar kwararar 'yan gudun hijira da bakin h...
Rating :
5