'Yan sandan Isra'ila sun bayyana cewa, sun hana Falasdinawa 'yan kasa da shekaru 50 shiga Masallacin Aksa mai girma.
An dauki wannan mataki ne sakamakon jifa da duwatsu da matasan Falasdinawa suka yi kan 'yan sandan na Isra'ila.
Kungiyar 'yantar da Falasdinawa ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu, Isra'ila ta kama Falasdinawa dubu 90,000 wadanda suka yi yunkurin shiga Masallacin na Aksa mai shekaru sama da dubu 2.
An bayyana cewa, dubu 12,000 daga cikin wadanda Isra'ilan ta kama yara ne kanana.
Title :
Isra'ila na ci gaba da zaluntar Falasdinawa a Baitul Makdis
Description : 'Yan sandan Isra'ila sun bayyana cewa, sun hana Falasdinawa 'yan kasa da shekaru 50 shiga Masallacin Aksa mai girma. An dauki w...
Rating :
5