Ingila tana daf da rasa gurbi daya daga cikin hudun da
take da su a gasar cin kofin zakarun Turai a 2017-18,
idan ta ci gaba da kasa taka rawa a gasar.
Kungiyoyin Ingila sun kasa kaiwa wasan daf da na kusa
da karshe a shekaru biyu a jere a gasar wasannin.
Ma'aunin da ake auna kwazon kasashe a fagen tamaula
da aka yi a shekaru biyar ya nuna cewar Ingila tana
mataki na uku, biye da Spaniya a mataki na daya sai
Jamus ta biyu.
Italiya ce a matsayi na hudu, kuma kasashe ukun farko
ne ake baiwa gurbin kungiyoyi hudu da suke buga gasar
cin kofin zakarun Turai.
Title :
Ingila za ta rasa gurbi daya a gasar zakarun Turai
Description : Ingila tana daf da rasa gurbi daya daga cikin hudun da take da su a gasar cin kofin zakarun Turai a 2017-18, idan ta ci gaba da kasa taka ...
Rating :
5