BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Salatin Allah da amincinsa su tabbata ga Annabin da yafi kowa gudun duniya da tsantseni cikinta, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu albarka.
Hakika Shaitan (LA'ANANNE) ya riga ya san sharrin duniya da kuma gubar da soyayyarta take haifarwa a zukatan mutane. Son haka tunda shi makiyinmu ne sai ya Qawata ita duniyar acikin zukatan mafiya yawa daga cikinmu.
Sai suka tafi zuwa gareta suka nutsu da ita (kamar ba zasu mutu su barta ba).
Kai wasu ma har sun riketa sun chijeta da hakoransu, basu da niyyar sassautawa cikin son da suke yi mata.
Acikinta suke tsere da juna, suna Qin junansu saboda ita, suna yiwa Juna hassada, Kai har dai sai da suka cika ma Iblees burinsa akansu.
Tunda ya riga ya fada agaban Ubangiji yana cewa: "WALLAHI SAI NA QAWATA MUSU ACIKIN QASA, KUMA WALLAHI SAI NA DULMIYAR DASU BAKI DAYA"
(Suratul Hijri ayah ta 39).
Hakika mafiya yawanmu mu 'yan Adam akan haka muke. Sai dai 'yan Qalilan wadanda Allah ya tsaresu da Qarfin Qudurarsa.
Da ache mu mutane mun fahimci menene hakikanin ita duniya, Wallahi da ba zamu taba daukarta abakin komai ba, kuma da ba zamu samar mata da gurbi acikin zukatanmu ba. Kuma da ba zamu samar mata da gurbin ambato akan harsunanmu ba.
Allah wanda ya halicci duniya da kayan cikinta shine ya gaya mana hakikarta. A inda yaje cewa:
"KUYI SANI CEWA ITA FA (RAYUWAR) DUNIYAR NAN BA KOMAI BACE IN BANDA WASANNI, DA WARGI, DA QAWACE-QAWACE, DA ALFAHARI ATSAKANINKU, DA NEMAN YAWAITUWA (DON YIN ALFAHARI) ACIKIN DUKIYA DA 'YA'YA".
(Suratul Hadeed ayah ta 20).
Idan dai haka rayuwar nan ta duniya take, wato wasa ne da WARGI, da Qawace-Qawace, to lallai mai hankali shine wanda ya dauketa ba komai ba, kuma ya mayar da ita tamkar wata gona ce wacce zai noma abinda zai ci alahirarsa.
Don haka ne Ubangiji yayi kiranmu da babbar murya. Yana cewa :
"KUYI TSERE ZUWA GA (SAMUN) WATA GAFARA DAGA UBANGIJINKU, DA KUMA WATA ALJANNAH WACCE FADINTA KAMAR FADIN SAMMAI DA QASSAI.
AN TANADAR DA ITA NE DOMIN WADANDA SUKAYI IMANI DA ALLAH DA MANZANNINSA".
(Hadeed ayah ta 21).
Lallai ne mu tashi tsaye mu zage damtse wajen neman Yardar Allah ta hanyar guje ma duniya. Da kuma kiyaye afkawa cikin Kogin Sonta wanda ba'a tsallakewa lafiya.
'Yan uwa ku dubi irin manyan laifukan da yanzu mutane suke aikatawa saboda sun makance don son duniya.
'Dan Adam yana kashe 'dan uwansa don neman duniya..
- Dan Adam yana shan jinin 'Dan uwansa son neman abin duniya.
- 'Dan Adam yana tsafi son neman abin duniya.
Duniyar da duk dadin da zata baka baifi na shekaru hamsin ba, agarin nemanta ka jefa kanka cikin bala'in azaba na miliyoyin shekarun da basu da iyaka, acikin wutar Jahannama, ga duhu ga zafin azaba, ga bakin ciki marar yankewa.Ya Allah ka kiyayemu
Sai gobe kuma zamu shiga cikin hadisai muji irin gargadin da Manzon Allah (saww) yayi mana game da sharrin Son duniya.