Ko kasan cewa duk lokacin da matarka ta 'bata maka rai in dai kayi hakuri domin Allah, akwai wasu alkhairai da zasu sameka kamar haka:
1. Idan Matarka ta 'bata maka rai anan duniya, nan take Matayenka na gidan Aljannah suna mayar da martani agareta (Sai dai ba zakuji ba). Suna ce mata: "KE DA KIKE TA 'BATA MASA RAI, AI YA KUSAN DAWOWA ZUWA GAREMU (WATO ALJANNAH - WAJEN DA ZAI DAWWAMA CIKIN FARIN CIKI).
2. In har kayi hakuri domin Allah sai Allah ya rubuta maka lada mai dimbin yawa, ba tare da lissafawa ba. Allah yana cewa "ANA BAMA MASU HAKURI NE LADANSU BA TARE DA LISSAFI BA".
3. Idan kayi hakuri domin Allah, to nan take Allah zai zama naka. Wato Allah yana tare da masu hakuri.
4. Idan kayi addu'a, Allah zai amsa maka alokacin. Domin Allah yana saurin amsa addu'ar wanda aka zalunta. (Kaga zaka iya rokon Allah ya chanza halayenta, ko kuma ya chanza maka wacce tafi-ta alkhairi).
5. Allah zai daukaka darajarka aduniya da lahira saboda albarkacin hakurinka. (Hakuri, afuwa, basu Qara maka komai sai dai girma awajen Allah).
6. Ubangiji zai Qara maka yawan Matan da Za'a baka agidan Aljannah. Tunda zaka samu Qarin daraja a Aljannar, kenan zaka samu Qaruwar ni'imah acikinta.
It means idan da chan za'a baka mataye guda 70 a Aljannarka, may be yanzu kuma Allah zai ninninka maka yawansu saboda hakurin da kakeyi.
7. Aranar lahira Allah zai kiraka agaban dukkan halittu, sannan yace maka "KA SHIGA ALJANNAH TA DUK QOFAR DA KAKESO". (Haka Manzon Allah (saww) yace: "Duk wanda ya danne fushi, alhali yana da ikon zartar dashi, Allah zai kirashi aranar Alqiyamah agaban dukkan halittu, sannan yace masa SHIGA ALJANNAH TA DUK KOFAR DA KAKE SO").
Manzo (saww) ya san da haka, Shi yasa ya umurcemu da cewa : "KUYI HAKURI DA MATA".
Ya riga ya san cewa Su mata wasu irin halittu ne. Ba zaka rayu cikakkiyar rayuwa ba dole sai dasu. Idan kuma kana tare dasu sai sun rika muzguna maka.
Ga rashin godiyar Allah.
Ga rainin wayo.
Ga rainin hankali.
Ga taurin kai.
Ga tsananin kishi.
Ga Hayaniya.
Ga tsananin son duniya.
Ga rashin hangen nesa.
Amma duk da haka Iyayenmu ne su, Yayunmu ne, Qannenmu ne, Kuma 'ya'yanmu ne. Don haka muyi ta hakuri dasu.
DAGA ZAUREN FIQHU.