TAMBAYA TA 1710
*********************
Assalamu alaikum. Mal ya aiki ya kokari Allah ta taimaka ya kuma saka da alkhairi.
Mal ina da tambayce kamar haka, ya halarta mutum ya boye ma yarinyar da zai aura mastalarsa ta ciwon HIV?? Shin yaya hukuncin wadda yayi hakan??
Nagode.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Ai wajibi ne ma duk mutumin da zai yi aure, idan har yana dauke da wata babbar chuta ta musamman (Kamar irin su Anemia, Asthma, Diabetes, Hypertension) ya fito yayi bayani ma wacce zai aura. Kamar yadda itama dole ne ta bayyana masa idan tana dauke da wata chuta ta musamman.
Ballantana Idan kuma ya zamanto irin chutar da ake iya dauka ne ta hanyar Jima'i, to agaskiya bai halatta gareshi ya auri mace lafiyayya ba. Sai dai idan ita dinma tana dauke da irin chutar.
Shi Musulunci addini ne wanda yake kare lafiyar mabiyansa da kuma mutuncinsu da dukiyoyinsu. Don haka babu chuta, kuma babu chutarwa aduk cikin kowacce hulda zakayi.
Koda a bangaren kasuwanci ballantana zamantakewar aure.
Duk wanda ya boye ma Budurwarsa cewa yana dauke da chuta, kuma har akayi auren ahaka, To anan tana da za'bi. Zata iya zuwa kotu ta raba auren idan har bai tare da ita ba.
Idan kuma har ya riga ya shafa nata chutar, to anan zata iya yin Qararsa awajen hukuma domin neman hakkinta na illar da ya goga mata alhali yana sane.
WALLAHU A'ALAM.