Assalamu alaikum. Allah Ya kara ma mallam basira. Mallam ina da tambaya ne akan gira, wata take chemin 'wai taji wasu malamai sun ce mutum zai iya ragewa indai ba duka zai aske ba, toh ba haramun bane' Mallam mene ne gaskiyan al'amarin? Nagode, Allah saka da alkhairi.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Gaskiya ban san wajen da ta samo wannan fatawar ba. amma mu dai abinda muka samu daga Alqur'ani da Sunnar Manzon Allah (saww) shine ASKE GIRA, KO RAGETA, duk haramun ne.
Akwai hadisi wanda Imamul Bukhariy da Muslim suka ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (ra) yana cewa:
"ALLAH YA TSINE MA Mata masu yin shasshawa (tattoos) da kuma wadanda suke yiwa mutane shasshawar, DA WACCE TA ASKE GASHIN GIRARTA da kuma masu sanyawa ayi musu Wushirya don kwalliya. Masu chanza halittar Allah".
Sai wata mata daga Banu Asad ta tuhumeshi akan mai yasa zai ce haka? Sai yace "DON ME BA ZAN TSINE MA WADANDA MANZON ALLAH (SAWW) YA TSINE MUSU BA?".
(Sahihul Bukhary hadisi na 4604, 4886. Sahihu Muslim hadisi na 2125).
Kuma Abdullahi bn Mas'ud ya Qara da cewa "MASU YIN HAKA DOMIN KWALLIYA" (Wato kamar yadda matan zamanin nan sukeyi kenan).
Aduba cikin FAT'HUL BAARIY juzu'i na 10 shafi na 377 za'a ga yadda Alhafiz Ibnu Hajr Al-Asqalaniy ya fadada bayani akan mas'alar.
Babu sabani tsakanin Malamai akan haramcin aske gashin gira ko rageshi domin kwalliya. Domin yin hakan kamar chanza halittar Allah ne. Kuma Manzon Allah (saww) ya tsine ma duk masu yin haka .
Aduba TAFSEERUL QURTUBIY juzu'i na 5 shafi na 392 don Qarin bayani.
WALLAHU A'ALAM.