TAMBAYA TA 1728
*********************
Assalamu alaikum. Allah shi gafarta Malam. Menene hukuncin Mutumin da ya sadu da matarsa alhali awajen aikin Hajji, Alhali ya riga yayi haramar aikin hajjin? amma saduwar ta faru ne kafin ranar Arfa.
Allah ya saka da alkhairi. Allah ya baka ikon amsa wannan tambayar.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Duk Mutumin da yayi Jima'i da iyalinsa alhali yana cikin Haramar aikin Hajji, kuma kafin tsaiwar arfah, To hakika ya aikata laifi babba.
Hukuncinsa awajen Imamu Malik da Imamu Ahmad da Shafi'iy, shine wajibi ne yayi hadaya da babbar dabba kamar Rakumi kenan ko Saniya.
An tsananta masa Kaffarar ne saboda girman laifin da ya aikata. Kuma Malaman Sunce zai je ya Qarasa sauran ayyukan Hajji har zuwa karshe. Kuma Wajibi ne ya sake dawowa ashekara ta gaba domin maimaita aikin Hajjinsa. Kuma Wajibi ne araba tsakaninsa da matar tasa idan sun sake dawowa domin maimaitawar.
Irin wannan ta ta'ba faruwa azamanin Sahabban Manzon Allah (saww). Wani mutum ya aikata irin haka sai Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) yace masa :
"KU QARASA AIKIN HAJJINKU, KU KOMA GARINKU. IDAN SHEKARA TA DAWO SAI KU SAKE FITOWA AIKIN HAJJI. IDAN KUNYI HARAMA SAI KU TABU DA JUNA. KAR KU SAKE HADUWA HAR SAI BAYAN KUN GAMA AIKIN HAJJINKU KUN YANKA HADAYA".
(Imamul Baihaqiy ne ya ruwaito hadisin da Isnadi Sahihi).
Ita ma Matar tasa Wajibi ne tayi Kaffarar yanka Hadayar Rakumi ko Saniya din. In dai ita ce taja hankalinsa har suka aikata wannan laifin bisa sin ranta.
Amma idan tilasta mata yayi, to babu kaffarah akanta.
WALLAHU A'ALAM.