BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Salati da tasleemi su tabbata ga Fiyayyen Makusantan Allah, Shugabanmu Annabi Muhammadu, Da iyalan gidansa tsarkaka hasken Al'ummah da sahabbansa shiryayyu da masu biye musu har zuwa ranar Qarshe.
Karatunmu na yau zamu yishi ne akan LAYYA DA HUKUNCE HUKUNCENTA.
SUNANTA : ADH-DHAHIYYAH ko kuma UDH-HIYAH, mu kuma da hausa muke cewa LAYYA. Abinda ake nufi da ADH-DHAHIYYAH, KO KUMA UDH-HIYYAH, shine dabbar da za'a yanka din.
Wato kamar rakumi ko saniya ko rago ko tinkiya ko Akuya wanda za'a yanka da niyyar ibadah da neman kusanci ga Allah (swt).
MATSAYINTA ACIKIN SHARI'AR MUSULUNCI :
Allah ne da kansa ya shar'anta ta a inda yake cewa -Acikin Suratul Kawthar:
"Hakika mun baka tafkin Alkawthar. Don haka kayi Sallah saboda Ubangijinka. Kuma kayi yanka".
(ayah ta 1 da ta 2)
Kuma ya tabbata acikin hadisi cewa Manzon Allah (saww) yayi layya, kuma Sahabbansa sunyi. Kuma dukkan Musulmai sun hadu akan haka.
FALALARTA:
==========
Imam Tirmizy ya ruwaito hadisi daga Sayyidah Aisha (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"BABU WANI AIKIN DA 'DAN ADAM ZAI AIKATA ARANAR EIDI WANDA YAFI SOYUWA AWAJEN ALLAH FIYE DA ZUBAR DA JINI (WATO LAYYA).
"HAKIKA WALLAHI ITA (DABBAR LAYYAN) ZATA ZO ARANAR ALKIYAMA TARE DA GASHINTA DA KAHONTA DA KOFATONTA.
KUMA JININTA YANA SAMUN MATSAYI GA ALLAH TUN KAFIN YA ZUBA A QASA. DON HAKA KU KYAUTATA NIYYARKU".
HUKUNCINTA:
**************
Hakika layya sunnah ce mai karfi daga cikin sunnonin Manzon Allah (saww).
Kuma an karhanta Qin yinta mutukar dai mutum yana da ikon yi. Saboda hadisin da Bukhary da Muslim suka ruwaita daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace:
Manzon Allah (saww) yayi layya da raguna Manya guda biyu masu fari da baki ajikinsu, kuma masu Qaho.
Ya yankasu da hannunsa, yayi basmala, kuma yayi kabbara.
Sannan akwai hadisin da Muslim ya ruwaito daga Sayyidah Ummu Salamah (ra) Daga Manzon Allah (saww) :
"IDAN ZUL HIJJAH YA KAMA, KUMA 'DAYAN CIKINKU YANA NUFIN ZAI YI LAYYA, TO KAR YA YANKE WANI ABU DAGA GASHIN KANSA KO FARCENSA".
Malamai sunce wannan hadisin ma kadai hujjah ne abisa Sunnantakar yin layyah.
An ruwaito cewa Sayyiduna Abubakar da Umar (ra) basu yima Iyalansu layyah (na kansu kadai suke yi) don kar mutane su dauki hakan amatsayin wajibi ne mutum sai yayi ma iyalansa bayan yayi ma kansa.
SHIN TAKAN ZAMA WAJIBI AKAN MUTUM KUWA?
-------------------------------------------------
Eh takan zama wajibi akan duk wanda yayi bakancen yinta. Kamar mutum yace "wallahi indai Allah ya bani 'Da Namiji to bana sai nayi layya"
To wannan Wajibi ne akansa sai yayi layyar mutukar dai sharadin ya cika.
Sannan takan zama wajibi akan duk wanda ya ware wata daga cikin dabbobinsa, yace WANNAN NA BAMA ALLAH NE.
To wannan ya zama wajibi sai yayi layyar. Kuma koda ya mutu sai 'yan uwansa sunyi masa amadadinsa.
Amma shi Imamuna Malik (rah) yace indai ka sayi wata dabba musamman da niyyar zakayi layya ne da ita, to wajibi ne sai kayi layyar nan da ita.
HIKIMAR DA TAKE CIKINTA:
***************************
Allah ya shar'anta ta ne ga al'ummar Musulmai domin su rika tunawa da Annabi Ibraheem (as). Kuma domin yalwatawa agaresu atsakaninsu aranar Eidi.
Kamar yadda Manzon Rahama (saww) yake cewa :
"Su wadannan kwanakin ci da sha ne, da kuma zikirin Allah (Azza wa Jalla).
DA WADANNE DABBOBI NE AKE YINTA?
***************************************
Ana yin layya ne da Rakumma ko Shanu ko Tumaki da Awakai.
Bai halatta ayi da waninsu ba.
Kamar yadda Allah yake cewa:
"DOMIN SU AMBACI ALLAH ABISA ABINDA YA AZURTASU DASHI DAGA CIKIN DABBOBIN NI'IMA".
(suratul Hajji ayah ta 34)
* Ya Halatta ayi da rago 'dan wata shida (6 months) zuwa sama.
* Ya halatta ayi da 'Akuya ko bunsuru dan Shaekara guda zuwa sama.
* Ya halatta ayi da Saniya ko Bijimi 'dan shakara biyu zuwa sama.
Ya halatta ayi da rakumi dan Shekara 5 zuwa sama.
Malamai sunce da dabba namiji da dabba mace duk daya ne wajen yankan. In dai sun kai shekarun da aka fada.
Nan zamu dakata sai anjima insha Allahu zamu karasa wannan karatun saboda muhimmancinsa awannan lokacin.