Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce mutane bakwai ne suka mutu sakamakon harin bam da aka kai a sansanin 'yan gudun hijra da ke Yola a jihar Adamawa.
Lamarin ya auku ne sansanin 'yan gudun hijira da ke Malkohi a cikin Yola.
Babban jami'in watsa labarai na hukumar, Sani Datti, ya ce mutane 20 kuma sun jikkata.
A cewar sa, an bai wa bakwai daga cikin wadanda suka jikkata magunguna, kana aka sallame su; yayin da mutane 13 -- cikin su har da jami'an hukumar guda hudu -- ke ci gaba da samun kulawa a asibitin Tarayya da ke Yola.
Daruruwan mutane ne ke zaune a sansanonin kula da 'yan gudun hijirar sakamakon aika-aikar da 'yan Boko Haram suka yi.
A baya dai kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a garin na Yola.
Title :
Harin Bam A Sasanin Ya Gudun Hijira Da ke Adamawa
Description : Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce mutane bakwai ne suka mutu sakamakon harin bam da aka kai a sansanin 'yan gudun hijra ...
Rating :
5