Hukumar aikin Hajji ta gwamnatin Najeriya ta tabbatar da mutuwar maniyyata 'yan Najeriya 6 yayin hatsarin da ya auku a Harami ranar Juma'a, inda mutane 107 suka mutu.
Huɗu daga cikin maniyyatan da suka mutu 'yan jihar Gombe ne, ɗaya daga jihar Kaduna, ɗaya kuma daga jihar Katsina.
An gano mamatan ne dai cikin wadanda hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwarsu da aka ajiye gawarwakinsu a asibitoci dake birnin Makkah.
Tuni dai aka sanar da dangin wadanda suka mutu a hatsarin.
Tuni dai hukumomin Saudiyyar suka bada umarnin gudanar da cikakken bincike dangane da hatsarin da ya auku yayin da wata ƙugiyar ɗaga kaya mai nauyi ta faɗo kan masallacin Haram.
Bana 'yan Najeriya 67, 000 ne ake sa ran zasu yi aikin Hajjin.