Android ba kamar sauran wayoyi bane, domin ita an tsarata da manyan kaya, sannan da yawan application wannan tasa masu ita suke ta kuka da ita wajen jan chaji da jan kudi, to ga wasu hanyoyi da zaka rage mata jan chaji na batir dinta.
1. Ka bude"Menu"sannan ka nufi"Setting"saika latsa"developer's options"sannan ka tafi can kasa, domin duk wani seti na wayar yana wurin saika latsa"Background process limit"zaka ganshi yana"standard limit"wato bashida adadin yawan app da wayar zata bude lokaci daya, to amma saika takaita, misali ta rika bude guda biyu, sabanin da wajen goma suna budewa suna aiki. Wannan zaisa batir naka yayi kwari, amma wannan baduk android keda wannan ba sai dai version 4.0.
Bayan ka seta wannan kayi restart na android naka, domin ta fara aikinta nan take.
2. Ka rika rufe bluetooth naka, kuma ya rika zama a hide, duk da android ta inganta wannan bangaren ta yadda koda ka bude second 120 yake ya koma hide da kansa. Ako wacce waya haka yake.
3. Ka rika rufe WI-FI naka da Hosport naka domin barinsu abude suna jan caji, domin duk abinda yake search kuma yayi connect to dayan biyu
* Ko dai yaja caji kadai
* Ko kuma yaja kudi da caji. Ako wacce waya haka yake, indai akwaishi.
3. Ka rage hasken screen na wayarka, domin yinsa da yawa, yana jan chaji, zaka gane haka, idan ka duba hasken BB dana LG, Ita BB zaka ganshi da haske sosai, kuma fari ko kuma mai Light haka, LG zaka ga nata da dan duhu, domin wanda ya saba aiki da BB idan ya kalli LG zaiga yana-yana yake kallo wayar ta yi masa duhu, mai amfani da LG idan ya kalli tayi masa haske dayawa. Zaka iya akowacce waya
4. Ka rage lokacin da haske yake dauka, domin yana jan caji, misali daga 15s, zuwa 5s. Wannan yana aiki aduk sauran wayoyi
5. Karinka rage mata network yayin da zakayi chat ko binciken labarai, amma ka bude shi duka idan kasan zakayi download, domin canzashi kaje"Setting"sai"Data&Sync"ka shiga saika latsa"background data