Assalamu Alaikum, gaisuwa me tarin yawa tare da fatan Alhairi da fatan malam yana cikin koshin lafiya, Allah yasa haka Ameeen!
Malam dan Allah a taimaka a amsamun tambayan nawa shine:
*mal, shin ya halatta dan'kasuwan da ke zuwa kasuwan kauye yin kasuwanci yayi KASARU, nisan kauye yakai tafiyan 1hr30m a mota??
*maganin ciwon kirji ne nake bukata, kirji nane yakemun ciwo wato da zaran na dan kwanta dan na huta sai naji ya fara mun ciwo amma idan na tashi sai naji ya daina?
*In yawan jin yunwa, wato da zaran ina gidan in naci abinci bana kai minti 15 sai naji ina jin yunwa sosai?
Nagode daga dalibin ka Luqman
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Eh ya halatta kayi Qasaru idan tafiyar takai wannan zangon, to tabbas nisan zai kai yadda Malaman Fiqhunmu Malikiyyah suka Qayyade din nan. Kuma tunda tafiyar kasuwanci ne, ba tafiyar sa'bon Allah bane, ai ya halatta kayi Qasaru acikinta.
Dangane da saurin jin yunwa da kuma ciwon Qirji. da yake damunka, ka nemi Man Habbatus sauda mai kyau na Kamfanin Hemani ko 'Dan Misra, Ka rika zuba cokali guda a ruwan Shayin Na'a-Na'a kana shansa da zuma.
In sha Allahu koda Ulcer ne je damunka zaka samu sauki.
WALLAHU A'ALAM.