Assalamu alaikum. Dafatar Malam kana lafiya
kaida iyalanka.
Malam tambayata 2 anan:
1. Shin Mutum zai iya auren matar kaninsa bayan
mutuwarsa?
2. Shin Mace zata iya auren mijin kanwarta idan ta
rasu? Na gode. Daga Aboubakr
Alkali.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Eh duk wadannan da ka lissafa, aure ya halatta atsakaninsu. Mutukar dai basu tare da ita waccen din.
Qulla irin wadannan auren yana da amfani saboda dorewar zumunci da kuma kulawa da yaran da ita mai rasuwar ko kuma shi mai rasuwan ya bari.
WALLAHU A'ALAM.