TAMBAYA TA 1713
*********************
Asslamu alaikum, da fatan Allah ya saka wa malam da alhairi. Malam tambaya ta itace; mai gidanmu ne ko yaushe shugaban ma'aikatarmu ya bashi aiki ko sayen wasu kaya sai ya wakiltamu, domin ya taimaka mana sai yace mu Qara wani abu daga cikin kudin, mafi yawan lokutta bamu san da maganar aikin ko sayen kayan ba. To malam mu munci halal kenan?
kuma bazamu iya ce mashi baza muyi ba, malam abinda yasa nayi wannan tambayar don ni kadaine musulmi. ina neman mafita.
Nagode.
musa j.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Hakika yin haka ya zama ZAMBA cikin aminci kenan. Domin kuwa Gwamnati ta amince daku ne shi yasa ta doraku bisa wannan aikin.
Don haka bai halatta gareku ku rika yin Qari acikin kudin ba. Tunda yin hakan ya zama ha'inci. Kuma Allah yana yin azaba ga masu yin ha'inci.
Bai kamata ku bada hadin kai ga wannan Ubangidan naku ba. Domin Allah yace : "KAR KUYI TAIMAKON JUNA CIKIN SA'BON ALLAH DA KETARE IYAKOKI".
Kuma Manzon Allah (saww) yace: "BA'A YIN BIYAYYA GA WANI MAHALUKI CIKIN SA'BON ALLAH".
Mafi alkhairi gareka shine kaji tsoron Ubangijin da ya halicceka. Ka sanya tsoronsa azuciyarka fiye da tsoron kowa..Koda zasu koreka daga kan wannan aikin, Allah zai baka wanda yafi shi.
Allah yana cewa: "DUK WANDA YAJI TSORON ALLAH, TO ALLAH 'DIN ZAI SANYA MASA MAFITA. KUMA ZAI AZURTASHI TA INDA BA YA TSAMMANI. DUK WANDA YA DOGARA GA ALLAH, TO SHINE MAI ISAR MASA".
Kayi kokari ka tsarkake hanyar cin abincinka. Domin wannan Qarin da kukeyi haram ne. Bai halatta gareku ba.
WALLAHU A'ALAM.