Hukumomin Saudiyya sun kare sukar da ake yi musu dangane da yadda suke gudanar harkokin aikin Hajji.
Hakan na zuwa ne bayan hatsarin da ya halaka mutane fiye da dari bakwai a hanyar zuwa Muna.
Wata sanarwa daga ma'aikatar kiwon lafiya ta Saudiyyar ta sake nanata zargin cewa, kin kiyaye ka'idoji da aka shimfida na daga cikin dalilan da suka haddasa hatsarin.
Sai dai Iran ta ce, kamata yayi Saudiyya ta amince da gazawarta wajen gudanar da aikin Hajjin.
'Tattara adadi'
Ana ci gaba da kokarin tantance asalin mutanen da suka mutu a turmutsutsun da ya faru, inda sama da mutane dari bakwai suka rasu a ranar Alhamis.
Wadanda suka rasa rayukan na su 'yan kasashe ne da dama da suka hada da Nigeria da Nijar da Kamaru da Iran da Turkiyya da Indiya da Indonesia da ma wasu kasashen Afirka.
Wani jami'i a Pakistan ya ce har yanzu ba a ga sama da mahajjatan kasar su fiye da 200.
Saudiyya ta sha alwashin gudanar da bincike kan lamarin.
Title :
Gwamnatin Saudiyya ta kare kanta
Description : Hukumomin Saudiyya sun kare sukar da ake yi musu dangane da yadda suke gudanar harkokin aikin Hajji. Hakan na zuwa ne bayan hatsarin da ya ...
Rating :
5