IKRIMAH ya karbo hadisi daga Ibnu 'Abbas (ra) yana cewa:
"Wasu mutane daga cikin Sahabban Manzon Allah (saww) sun zauna suna jiransa, chan sai ya fito. Har sai da yazo kusa dasu sai yaji suna Muzakarah atsakaninsu.
Sai ya saurari zancensu, yaji wani daga cikinsu yana cewa:
"Abin mamaki!! Allah ya riki bada'di (wato Khaleel) daga cikin halittunsa. Domin Annabi Ibraheem shine BADA'DIN ALLAH.
Sai kuma wani daga cikinsu yace "Ai wannan bai zama abin mamaki ba, kamar zancen nan da Allah yakeyi da Annabi Musa (as).".
Sai kuma wani daga cikinsu yace: "To ai Annabi Eisa (as) Shi Kalmar Allah ne, kuma Ruhin Allah".
Sai wani kuma daga cikinsu yace: "To ai ga Annabi Aadam nan wanda Allah ya zabeshi".
Daga nan Sai Manzon Allah (saww) ya fito garesu yace musu "DUK NAJI ZANCENKU DA KUMA MAMAKIN DA KUKEYI CEWA ANNABI IBRAHEEM SHINE BADA'DIN ALLAH, EH HAKANE. HAKANAN ANNABI MUSA (AS) YANA ZANCE DA ALLAH. EH HAKANE".
"KUMA ANNABI EISA (AS) RUHINSA NE KUMA KALMARSA NE. EH DUK HAKANE. KUMA ANNABI AADAMU (AS) ALLAH YA ZABESHI. EH HAKANE".
"KU SAURARA!!! HAKIKA NINE HABIBULLAHI (MASOYIN ALLAH). KUMA BAN FADA DON ALFAHARI BA".
"KUMA NINE MAI DAUKAR LIWA'UL HAMDI (TUTAR GODIYA) ARANAR ALKIYAMAH. DA ANNABI AADAMU DA DUK WANDA KE QASANSA, DUK SUNA KARKASHINTA (WANNAN TUTAR). KUMA BAN FADA DON ALFAHARI BA".
"KUMA NINE FARKON WANDA ZAI NEMI CHETO, KUMA FARKON WANDA ZA'A BAMA CHETO ARANAR ALQIYAMAH. BAN FADA DON ALFAHARI BA".
"NINE FARKON WANDA ZAI MOTSA KYAUREN GIDAN ALJANNAH, BA ALFAHARI NAKE YI BA".
"ALLAH ZAI BUDE MIN, YA SHIGAR DANI CIKINTA TARE DA TALAKAWAN MUMINAI. KUMA BAN FADA DON ALFAHARI BA".
"KUMA NINE NAFI DUKKAN MUTANEN FARKO DA MUTANEN QARSHE, GIRMAN MATSAYI AGUN ALLAH. KUMA BAN FADA DON ALFAHARI BA".
Aduba cikin TUHFAH, hadisi na 6,095. Da kuma AL-IT'HAF hadisi na 8,535.
Na tabbata cewa wannan hadisin DOLE zai faranta zukatan Masoyan Sayyiduna Rasulullahi (sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam).
Amma tukwicin da Mai Zauren Fiqhu yake nema awajenka shine ka tsaya kayi ma Annabinmu Salati da Tasleemi, kuma ka roka mana Qarin Kusanci gareshi, da kuma Tabbatuwa bisa tafarkinsa har Qarshen Numfashinmu.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (4).