Gareth Bale ya dawo atisaye domin buga wa Wales wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za ta yi a cikin watan Oktoba.
Bale ya ji rauni ne a karawar da Real Madrid ta doke Shakhtar Donetsk ranar 16 ga watan Satumba a gasar cin kofin zakarun Turai.
Dan wasan mai shekaru 26, bai buga wa Real Madrid wasanni uku ba, sakamakon raunin da ya ji, zai kuma dawo da buga mata tamaula a karawar da za ta yi da Atletico Madrid ranar 4 ga watan Oktoba.
Wales za ta kara da Bosnia-Herzegovina a Zenica ranar Asabar 10 ga watan Oktoba, sannan ta karbi bakuncin Andorra a ranar Talata.
Title :
Gareth Bale Ya Dawo Baya Jinya
Description : Gareth Bale ya dawo atisaye domin buga wa Wales wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za ta yi a cikin watan Oktoba. Ba...
Rating :
5