Direbobin motocin dake ratsa dajin falgore a kan hanyarsu ta zuwa Jos daga Kano, sun koka da yawan fashi da makami da suke fuskanta a kan hanyar.
Direbobin sun ce janye shingayen sojojin da aka yi a titin da ya ratsa ta dajin, ya bai wa 'yan fashi damar cin Karen su ba babbaka kusan ko yaushe
Su ka ce hakan na jefa su cikin halin dar-dar a duk lokacin da zasu ratsa dajin.
To sai dai rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce za ta samar da jami'an tsaro a cikin dajin, domin magance yawan fashin da ake fuskanta.
Title :
Fashi Yana Karuwa A Dajin Falgore
Description : Direbobin motocin dake ratsa dajin falgore a kan hanyarsu ta zuwa Jos daga Kano, sun koka da yawan fashi da makami da suke fuskanta a kan ha...
Rating :
5