Yan uwa ga wasu Hadisai nan Sahihai daga Manzon Allah (saww) wadanda zasu bayyana mana kadan daga cikin falalar wannan ranar da muke ciki, da kuma Azumin da mukeyi na yau:
1. Manzon Allah (saww) yana cewa: "AZUMIN RANAR ARFAH NA NEMA AGUN ALLAH CEWA YANA KANKARE (ZUNUBAN) SHEKARAR DA TAKE KAFINTA, DA WACCE ZATA ZO ABAYANTA".
(Muslim ne ya ruwaito)
2. Manzon Allah (saww) yace:
"MAFIFICIYAR ADDU'A ITA CE ADDU'AR DA AKAYI TA RANAR ARFAH. KUMA MAFI ALKHAIRIN ABINDA NA FA'DA NI KAINA DA KUMA ANNABAWAN DA SUKE KAFIN NI, SHINE "LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADEER"
(Tirmidhy ne ya ruwaito).
3. Manzon Allah (saww) yace:
"BABU WATA RANAR DA ALLAH YAFI 'YANTAR DA BAYINSA DAGA WUTA FIYE DA RANAR ARFAH.
KUMA ALLAH YANA KUSANTOWA GARESU (WATO WADANDA SUJE TSAYE AKAN DUTSEN ARFAH).
HAR MA YANA YIWA MALA'IKU ALFAHARI DASU. YANA CEWA : "SHIN MENENE (WADANNAN BAYIN) SUKE BUKATA?".
(Muslim ne ya ruwaito hadisin).
4. Nana Aisha (rta) tana cewa:
"ACIKIN SHEKARA BABU WATA RANAR DA NAFI SON INGA NA AZUMCETA KAMAR RANAR ARFAH".
(Musnadul Ja'ad, hadisi na 512).
Title :
Falalar Azumin Ranar Arfah
Description : Yan uwa ga wasu Hadisai nan Sahihai daga Manzon Allah (saww) wadanda zasu bayyana mana kadan daga cikin falalar wannan ranar da muke ciki, d...
Rating :
5