A yunkurin yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya karkashin shugabancin gwamnatin Muhammadu Buhari. Hukumar EFCC mai yaki da al’mundahana a kasar na ta ci gaba da fafata aikin kaiwa ga gaci.
Yanzu haka reshen ofishin shiyyar Arewa maso Gabas da ke jihar Gombe, sun kai samame sun kuma cafke wani mataimakin shugaban jami’ar Jihar Adamawa Farfesa David Shel da kuma shugaban jami’ar Manjo Janar Haladu Hananiya mai ritaya.
Kamar yadda kakain hukumar a yankin ya shaidawa Wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad cewa, an kama mutanen ne bisa zargin almundahana da kuma facaka da dukiyar gwamnati.
Kakakin ya yi cikakken bayanin yadda wasu Miliyoyin kudi suka ga tasku wajen amfani da su da makamantan wadannan abubuwa. CIkakken jawabin na cikin wannan rahoto cikin murya da ke kasa.
Title :
EFCC ta cafke shugaban Jami’ar Adamawa
Description : A yunkurin yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya karkashin shugabancin gwamnatin Muhammadu Buhari. Hukumar EFCC mai yaki da al’mundahana ...
Rating :
5