Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kwanankin kungiyar Boko Haram na gab da karewa.
A cikin sakonsa na tana jama'ar kasar murnar Babbar Sallah, shugaba Buhari ya ce lokacin tashin hankali da fargaba da jama'a ke cikin yanzu a wasu sassan kasar za su zama tarihi nan bada dadewa ba.
Ya ce sojojin kasar ba za su sassauta ci gaba da fatattakar mayakan Boko Haram har sai an samu nasara akan su.
Shugaban ya umurci hukumomin tsaro a kasar da su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a a lokacin babbar Sallar.
Ya kuma yi ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su sakamakon hare haren 'yan bindiga a wasu sassan kasar kwanakin baya.
Title :
'Kwanan Boko Haram ya kusa karewa'
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kwanankin kungiyar Boko Haram na gab da karewa. A cikin sakonsa na tana jama'ar kasar murnar B...
Rating :
5