Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya, IOM ta ce sama da mutane miliyan biyu ne suka rasa muhallansu a arewa maso gabashin Nigeria sakamakon ayyukan 'yan Boko Haram.
Hukumar IOM ta ce ta sake nazari kididdigar da ta yi a baya ne, inda ta ce mutane miliyan daya ne suka rasa wurin zama dalilin hare-haren Boko Haram.
Hakan na zuwa bayan da alamu ke nuna cewar rundunar sojin Nigeria na samun galaba a kan mayakan Boko Haram.
Ko a cikin wannan makon ma, sai da rundunar sojin saman kasar ta yi ikirarin cewa ta yi luguden wuta a kan wuraren da 'yan Boko Haram suka boye a dajin Sambisa.
Dubban mutane aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon rikicin Boko Haram a cikin shekaru shida a Nigeria
Title :
Boko Haram ta raba mutane miliyan biyu da muhallinsu
Description : Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya, IOM ta ce sama da mutane miliyan biyu ne suka rasa muhallansu a arewa maso gabashin Nigeria sak...
Rating :
5