Mayakan Boko Haram a kan kekuna sun kaddamar da hari a wani kauye a yankin Askira Uba da ke jihar Borno inda suka kona gidaje da dama.
Wata mata ta shaida wa BBC cewar 'yan Boko Haram din masu yawa sun je kauyensu mai suna Pumbum a ranar Lahadi, sannan suka yi ta harbe-harbe kafin su kona gidajen jama'a.
"Mayakan Boko Haram sun zo a kan keke sannan suka kashe mutane uku a cikin gidanmu. Sun yi ta harbe-harbe sannan suka kona mana gidaje," in ji Matar.
Ta kara da cewar "Sun kwashe kayan abinci da kuma awaki da kaji kafin su kona gidajenmu."
A cewarta sai da 'yan Boko Haram suka kwashe kusan sa'o'i hudu a kauyen, kafin sojoji su kawo mu su dauki.
A cikin makon da ya wuce ne rundunar sojin Nigeria ta yi zargin cewa wasu mutane masu karfin fada-a-ji a jihar Borno na yin zagon kasa a kokarin sojojin na kawar da kungiyar Boko Haram.
Haka kuma rundunar sojin ta ce mayakan Boko Haram 200 sun mi?a wuya, bayan da dakarun kasar suka diran ma sansanoninsu da ke garin Banki a jihar Borno a cikin makon da ya gabata.
Title :
Boko Haram ta kai hari a yankin Askira Uba
Description : Mayakan Boko Haram a kan kekuna sun kaddamar da hari a wani kauye a yankin Askira Uba da ke jihar Borno inda suka kona gidaje da dama. Wata...
Rating :
5