Rundunar sojin Nigeria ta ce mayakan Boko Haram 200 sun mika wuya, bayan da dakarun kasar suka diran ma sansanoninsu da ke garin Banki a jihar Borno.
Lamarin ya auku ne bayan da sojojin suka kwace iko da garin na Banki wanda ke kan iyaka da jamhuriyar Kamaru.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce 'yan Boko Haram din sun miƙa wuya ne bayan da aka ci karfinsu a garin Banki a ranar Alhamis.
Garin na Banki na da matukar muhimmanci ta fuskar kasuwanci ga kasashen Nigeria da Kamaru da kuma Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
A cikin 'yan makonnin nan dai, 'yan Boko Haram na shan luguden wuta daga hannun sojojin Nigeria abin da ke nuna alamun ana samun galaba a kansu.
'Yan Nigeria da dama za su so gani a zahiri a kan cewar ko tabbas mutanen da suka mika wuya 'yan Boko Haram ne, ba wai fararen hula bane wadanda 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su.
bbchausa
Title :
'Yan Boko Haram 200 sun mika wuya
Description : Rundunar sojin Nigeria ta ce mayakan Boko Haram 200 sun mika wuya, bayan da dakarun kasar suka diran ma sansanoninsu da ke garin Banki a ji...
Rating :
5