Mutane a kalla 10 sun rasu sannan wasu fiye da 100 sun ji raunuka sakamakon fashewar bama-bamai a lardin arewa mai nisa a Kamaru.
Bayanai sun ce bam din farko ya tashi ne a kusa da sansanin jami'an tsaro, a yayinda daya bam din ya fashe a kusa da kasuwar kauyen Kerawa.Rahotanni sun nuna cewa 'yan kunar bakin wake ne suka kai hari a kauyen da ke kusa da kan iyaka da Nigeria.
Ko a cikin watan Fabarairun bana ma sai da mayakan Boko Haram suka kaddamar da hari a kusa da kasuwar, lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama.
Ana zargin mayakan Boko Haram ne ke kai hare-hare a garuruwan da ke Lardin arewa mai nisa a Kamaru musamman na garin Maroua a watan Yuli inda mutane da dama suka hallaka.
A yanzu haka dai kasashen Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi da kuma Benin sun kafa rundunar hadin gwiwa domin murkushe 'yan Boko Haram.
Title :
Bam ya hallaka mutane 10 a Kamaru
Description : Mutane a kalla 10 sun rasu sannan wasu fiye da 100 sun ji raunuka sakamakon fashewar bama-bamai a lardin arewa mai nisa a Kamaru. Bayanai s...
Rating :
5