Yar Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Dakta Fatima Atiku Abubakar, kuma sabuwar Kwamishinar ma’aikatar lafiya ta jihar Adamawa ta ware wani kaso daga cikin albashi da alawus dinta domin gudanar da ayyukan lafiya a jihar.
Da ta ke amsa tambayoyi ga manema labarai jim kadan da karbar rantsuwar da ta yi da sauran Kwamishinoni 21, Dk. Fatima ta ce za ta yi da gaske game da batun harkar lafiya a jihar, don harkar na fuskantar kalubale mai girma.
“Amma ni ina cikin matukar farin ciki da Gwamna ya nada ni Kwamishiniyar ma’aikatar lafiya. Ma’aikata ce da take cike da kalubale, saboda matsalar ‘yan bindiga din nan ya haifar da matsaloli da dama a fannin lafiyar jama’ar jihar. Saboda wannan yanayin, zan maida albashi da alawus di na wajen aikin jin kan lafiya ga jama’ar jihar”, inji ta.
Cikin jawabin da ya gabatar wajen rantsar da Kwamishinonin, Gwamna Muhammad Bindow Jibrilla, ya bayyana cewa an zabo Kwamishinonin ne bisa dacewar da suke da ita a fannonin da aka nada su.
Don haka sai Gwamna Bindow ya bukaci Kwamishinonin da su hada hannu da shi wajen samar da ci gaba da canji mai ma’ana ga jama’ar jihar. Ya ce, kuma biyayyarsu ta koma ga yi wa jama’ar jihar aiki ne, ba shi ba.
“Biyayyarku ta zama ta jama’ar Adamawa ce, domin su ku ke wakilta,ba ni ba,” in ji shi.
Da take maida kalami a madadin Kwamishinonin, Kwamishiniyar ma’aikatar ilimi ta jihar, Uwargida Kaletapwa Farauta, ta gode wa Gwamnan da ya nada su wadannan mukamai. Ta tabbatar da cewa ba za su ba mara da kunya ba.