Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce tawagarsa za ta iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba a gasar zakarun Turai duk da cewar kawo yanzu kungiyar bata samu maki ko daya ba a gasar.
Hakan na zuwa ne bayan da Arsenal ta sha kashi a hannun Olympiakos da ci uku da biyu a wasan da suka buga a filin Emirates.
Wasannin Arsenal biyu da ke tafe za ta hadu ne da Bayern Munich.
"Mu na cikin tsaka mai wuya amma babu matsala za mu kai gaci," in ji Wenger.
"Dole ne mu samu sakamako mai kyau tsakaninmu da Bayern Munich."
Sauran sakamakon wasannin da aka buga:
Barcelona 2 - 1 Bayer Leverkusen
Bayern Mun 5 - 0 Dinamo Zagreb
FC Porto 2 - 1 Chelsea
BATE Bor 3 - 2 Roma
Maccabi Tel Aviv 0 - 2 Dynamo Kiev
Lyon 0 - 1 Valencia
Zenit St P 2 - 1 KAA Gent
Title :
Ba mu fitar da rai kan Kofin Turai ba — Wenger
Description : Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce tawagarsa za ta iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba a gasar zakarun Turai duk da cewar kawo yanzu kungiyar ...
Rating :
5